Rasha ta shiga cikin sahun jerin kasashen da ke gogayyar samun izinin karbar kakuncin kofin nahiyar Turai a shekarar 2028 da kuma 2032, duk da dakatarwar da ita da aka yi mata biyo bayan mamayar da tayi a Ukraine.
A ranar Laraban nan ce dai hukumar shirya wasannin nahiryar Turai ta bayyana sunayen kasashen da suka nuna sha’awar su na karbar bakuncin gasar inda kasashen Rasha da Turkiya da Ingila da kuma Ireland ne dai za su yi gogayya wajen neman karbar bakuncin gasar na shekarar 2028.
A watan Satunba ne ake saran hukumar UEFA za ta sanar da kasar da zata amshi bakuncin gasar.
Rasha ita ce dai ta karbi bakuncin gasar kwallon kafa ta duniya a shekarar 2018 sannan aka tsaida gudanar da wasan karshe na lashe kofin zakarun nahiyar Turai a wannan shekarar a can, sai dai daga baya aka sauya saboda mamayar da ta yi a Ukraine.
Turkiya na saran karbar bakuncin gasar bayan da ta yi rashin nasara a wajen Jamus da zata amsa bakuncin gasar na shekarar 2024.
A wani labarin na daban Kungiyar agaji ta Oxfam ta yi gargadin cewa mutane kusan miliyan 28 a gabashin Afirka na fuskantar barazanar matsananciyar yunwa saboda tashin farashin kayayyaki da ya samo asali daga rikicin Rasha da Ukraine da kuma jinkirin saukar damunan bana .
Yakin Rasha da Ukraine
Har ila yau, kungiyar ta bayyana damuwa dangane da yadda hankalin kasashen duniya ya karkata kan yakin Rasha da Ukraine, lamarin da ya kai ga watsi kan matsalar karancin abinci da ake fuskanta masamman a gabashin Afirka.
Cikin sanarwa da ta fitar, Oxfam ta ce gidauniyar Majalisar Dinkin Duniya ta 2022 ta tarawa kasashen Habasha da Somaliya da Sudan ta Kudu kudaden agaji na tafiyar hawainiya, inda ya zuwa yanzu kashi 3 cikin ɗari kachal aka samu na dala biliyan 6 da ya kamata a samar.
Babban bala’i
A cewar darektan zartarwa na kungiyar Oxfam Gabriela Bucher, “Yankunan Habasha, Kenya, Somaliya, Sudan ta Kudu da sauran su na fuskantar babban bala’I, duk da cewa yankin na dakon ruwan sama cikin wannan watan, zai yi wuya sus amu cikakken murmurewa, muddun ba a dauki matakin gaggawa ba.