Fitacciyar ‘yar wasan tseren Najeriya Blessing Okagbare, ta gaza daukaka kara kan hukuncin haramcin shiga wasanni na tsawon shekaru 10 da kotun ladabtarwa a harkar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle AIU ta yanke mata.
Haramcin karin shekaru biyar ya hau kan ‘yar tseren ne kuma, bayan samun ta da laifin kin ba da hadin kai ga binciken da ake yi kan zarge zargen da ake mata.
A baya dai Okagbare ta yi barazanar daukaka kara kan hukuncin zuwa gaban kotun sauraron kararrakin wasanni a cikin kwanaki 30, wa’adin da ya wuce ranar 18 ga Maris da muke ba tare da ‘yar tseren ta dauki matakin ba.
A wani labarin na daban Rasha ta shiga cikin sahun jerin kasashen da ke gogayyar samun izinin karbar kakuncin kofin nahiyar Turai a shekarar 2028 da kuma 2032, duk da dakatarwar da ita da aka yi mata biyo bayan mamayar da tayi a Ukraine.
A watan Satunba ne ake saran hukumar UEFA za ta sanar da kasar da zata amshi bakuncin gasar.
Rasha ita ce dai ta karbi bakuncin gasar kwallon kafa ta duniya a shekarar 2018 sannan aka tsaida gudanar da wasan karshe na lashe kofin zakarun nahiyar Turai a wannan shekarar a can, sai dai daga baya aka sauya saboda mamayar da ta yi a Ukraine.
Turkiya na saran karbar bakuncin gasar bayan da ta yi rashin nasara a wajen Jamus da zata amsa bakuncin gasar na shekarar 2024.