Daya daga ciki lauyoyin da suke gudanar da shari’ar da gwamnatin kaduna ta shigar da shugaban mabiya darikar shi’a na najeriya, sheikh Ibrahim Zakzaky ya tabbatar da cewa a yadda suka karanci shari’ar da ake gudanarwa a kwai tabbacin kotun mai adalchi zata kori wannan kara kuma ta saki malamin da mai dakin sa kuma muna kara bama mabiyan malamin tabbacin cewa gaskiya zatayi halin ta a wannan shari’a.
Barrister Ishaq Adam wanda babban lauya ne kuma yana cikin tawagar lauyoyin karkashin jagorancin babban lauya Femi Falana SAN ya tabbatar da hakan ne a hirar sa da gidan jaridar ”Islam Times” inda yace kamar yadda muka gabatar da rokon mu tare da bayyan hujjoji gami bukatar kotu tayi ruling a kan ”NO CASE SUBMISSION” tabbatar muna ta tabbacin wannan shari’ar ta cika duk wasu sharudda da za’a tabbatar da rokon mu kun da cewa alkalin mai adalchi ne kuma bazai lura da interest din gwamnati ba zai yanke hukunci bisa ka’ida kamar yadda kundin tsarin mkulkin kasa ya bukace shi da yayi.
Shari’ar da jagoran mabiya harkar musulunci wadanda aka fi sani da ‘yan shi’a ta dauki hankalin muhumman mutane daga ciki da wajen najeriya kuma rahotanni sun tabbatar da cewa wasu gwamnatocinn kasashen ketare suna da interest a kan shari’ar wanda asakamakon hakan ne ma shari’ar take samun matsaloli na jan kafa gami da jinkiri nan da can.
Shi dai shugaban mabiya darikar shi’ar tare da matar malama zinatuddin suna fuskantar tuhumomi kusan goma sha biyar wanda ciki har da tuhumar hada kai da bata taimako wajen kisan wani babban soji a kaduna.
Tun a farkon shari’ar shugaban na mabiya darikar shi’a ya musanta zargin in da ya kira hakan a matsayin cin fuska ga shaksiyyar sa sa’annan yayi amfani da kalmomin turanci ma’ana ”rubbish and nonse” a matsayin amsa ga tambayoyin da kotu dayi masa wanda hakan yake nuni da cewa zarge zagen ba wasu abu bane illah soki burutsu kuma marasa makama balle tushe.