Rundunar ‘Yan sanda a jihar Agadas da ke arewacin Jamhuriyar Nijar ta tsare shugaban Karamar Hukumar Fashi tare da direbansa bayan gano kilogram fiye da 200 na hodar ibilis a cikin motarsa a ranar Lahadin da ta wuce a wani wurin binciken jami’an tsaro.
Bayan kusa da sa a daya jami’an hukumar suka tabbatar da abin da suke zargi,wato wasu harantatun abubuwan da aka saka a cikin manyan akwatina wadanda aka yi anfani da motar iko wajan jigilar su.
An dai kiyasta cewa, darajar kwayar ta kai biliyan 5 na kudin CFA.
Ya zuwa yanzu hukumomin’ ‘yan sanda na tsare da Sharou Sanda, shugaban Karamar Hukumar Fachi tare da matukinsa, yayin da ake ci gaba da neman wani mutun guda da ya hada baki da su, mutunen da bayanai ke nuna cewar kodawane lokaci za’a iya tasa keyarsu zuwa birnin Yamai.
Ko a ranar 7 ga watan Disamban 2021,sai da Hukumar Yaki da sha da kuma ta’ammuli da muggan kwayoyi ta yi kamen akalla kilogram 330 na wiwi tareda tsare mutun 10.
Tun bayan faduwar mulkin tsofon shugaban kasar Libiya Mouammar Khadafi, wani bangare na Saharar Agadas da ke arewacin Jamhuriya Nijar ya zama wanin yankin da masu fataucin muggan kwayoyi da makamai ke cin karansu ba babbaka ,duk da kokarin hukumomin kasar na tabbatar da tsaro a wannan yankin wanda ya raba iyaka da kasashen Libiya da Algeria da kuma Chadi.