An dage fafatwa tsakanin Everton da Newcastle a yau Alhamis saboda yadda ‘yan wasa ke fama da cutar Korona da kuma raunuka.
Yanzu haka dai, kimanin wasanni 16 kenan aka dage a gasar firimiyar Ingila a cikin wannan wata na Disamba, yayin da kuma alkalumma suka tabbatar da cewar, fiye da mutane 100 da suka hada da ‘yan wasa da ma’aikatan kungiyoyin kwallon kafar da ke taka leda a gasar ta Firimiya ne suka kamu da cutar Korona a cikin watan Disamba.
Sai dai duk da karuwar masu Korona a tsakanin ‘yan wasa, kungiyoyin da ke buga gasar Firimiya sun yi watsi da shawarar dakatar da kakar wasan da ake ciki zuwa wani lokaci a nan gaba, don dakile yaduwar cutar tsakanin ‘yan wasan.
Kungiyoyin dai sun tsaya kan cewa matukar kowacce daga cikinsu na da ‘yan wasa 13 lafiyayyu da kuma mai tsaron raga, to wasanni za su ci gaba da tafiya kamar yadda aka tsara.
A wani labarin na daban Masu ruwa da tsaki kan tamaula sun bayyana damuwa dangane da rage yawan ‘yan kallon da gwamnatin Faransa ta yi a filayen wasanni da zummar dakile yaduwar annobar Korona, matakin da suka ce zai rage armashin wasannin da ya dawo tun bayan rashin walwalar da suka fuskanta a shekarar 2020, lokacin da annobar ta kai kololuwa.
Wannan doka dai za ta shafe makwanni uku tana aiki, daga ranar 3 ga watan Janairu.
A ranar Juma’a 7 ga watan na Janairu kuma za a cigaba da wasannin gasar Ligue 1, bayan da sabbin matakan takaita walwala da taron jama’a suka fara aiki, wadanda za su shafi wasannin da za a kara tsakanin Lyon da Paris Saint-Germain a ranar 9 ga wata, wasa mafi girma a a karshen mako, sai kuma karawa tsakanin Lille da Marseille.
Idan kuwa aka tsawaita matakan dakile annobar ta Korona, hakan na nufin Real Madrid za ta buga gasar cin kofin zakarun Turai da PSG a zagaye na 2, da ya kunshi kungiyoyi 16 ranar 15 ga Fabrairu a gaban ‘yan kallon da yawansu ba zai wuce dubu 5 ba a birnin Paris.