Tauraron Real Madrid kuma dan wasan gaba na kungiyar Karim Benzema, ya zura kwallaye uku rigis a ragar Paris Saint Germain, kwallayen da suka yi sanadin ficewar kungiyar ta Faransa daga gasar cin kofin zakarun Turai ta bana.
A zagayen farko na karawar da suka yi a Faransa dai, PSG ce ta doke Madrid da kwallo 1-0, yayin da kuma a karawa da biyu Zakarun na La Liga suka lallasa PSG da kwallaye 3-1.
Bayan kimanin sa’a 1 da fara karawar da suka yi a daren ranar Laraba, mai tsaron ragar PSG Gianluigi Donnarumma yayi kuskuren da ya baiwa Benzama damar jefa kwallon farko.
Dan wasan gaban na tawagar kwallon kafar Faransa ya kara kwallo ta biyu da ta uku ne kuma a cikin mintuna biyu kacal, abinda ya sa aka tashi wasan Real Madrid na da jumillar kwallaye 3, PSG kuma 2.
A wani labarin mai kama da wannan Karim Benzema yana da yakinin cewa zai samu kuzarin da zai fafata a wasan kungiyarsa, Real Madrid da Paris Saint-Germain a wasan gasar zakarun nahiyar Turai in an jima a Talatar nan, bayan da ya yi jinyar rauni a kafarsa.
Benzema, wanda shine dan wasan da ya fi kowa saka kwallaye a raga a Real Madrid, inda ya ci kwallaye 24 a dukkan gasa, bai buga wa kungiyar tasa wasanni 3 ba tun bayan da ya fita daga fili yana dingishi a wasan da suka barje gumi da Elche 2-2 a ranar 23 ga watan Janairu.
Benzema ya ce fafatawarsa da kylian Mbappe a bangaren PSG wani abu ne na musamman a gareshi, duba da yadda ake ta rade radin zai koma Madrid, da kuma ganin cewa dukkanninsu su na yi wa tawagar Faransa wasa.
Bangarorin 2 za su hadu ne a filin wasa na Parc des Princes, kana su yi fafatawa ta 2 a Madrid ranar 9 ga watan Maris.