Akwai rade-radin cewa Cif Olusegun Obasanjo da tsofaffin sojoji sun watsar da Atiku Abubakar Tsohon shugaban na Najeriya ya na sha’awar shugabancin kasar nan ya bar Arewa a zaben 2023 Idan ‘Yan Kudu za su karbi shugabanci, ‘Yan takarar Obasanjo sun hada da Dr. Akinwumi Adesina.
Alamu su na nuna cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo da wasu tsofaffin sojojin kasa su na goyon bayan mulki ya koma kudu a 2023.
A ranar 14 ga watan Fubrairu 2022 ne jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa Olusegun Obasanjo da wasu abokan aikinsa su na da ‘yan takarar shugaban kasa.
8.4K Daga cikin wadanda suke marawa baya su karbi mulkin Najeriya a zabe mai zuwa akwai shugaban bankin nan na cigaban Afrika, Dr. Akinwumi Adesina.
Har ila yau ana kishin-kishin cewa manyan kasar su na tare da tsohon gwamna Peter Obi da kuma tsohon mataimakin shugaban CBN, Farfesa Kingsley Mohgalu.
Wani na kusa da tsohon shugaban Najeriyan da tsofaffin Janar na sojoji ya shaidawa jaridar cewa manyan kasar ba su tare da Atiku Abubakar a zaben na 2023.
An kawo maganar Farfesa Jega Ana kuma samun kishin-kishin cewa tsohon shugaban hukumar zabe na kasa watau INEC, Farfesa Attahiru Jega suke so a mataimakin shugaban kasa. “Shi Obasanjo ya na goyon bayan mulki ya koma kudu.
Mutanen da yake sha’awa sus amu mulki su ne; Akinwumi Adesina, Peter Obi da Kingsley Moghalu.” “A yankin Arewa kuma, ya (Obasanjo) na kaunar Attahiru Jega (tsohon shugaban hukumar INEC), ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa.”
IBB “Bai tare da Atiku Abubakar ko kadan. Ya na goyon bayan mulki ya bar Arewa.” – Majiyar.
Farfesa Jega ne ya jagoranci shirya zabukan da aka yi a 2011 da 2015. Bayan ya sauka daga mukaminsa, malamin jami’ar ya shiga siyasa domin kawo gyara.
Tambuwal ya dage Kun ji cewa domin ganin ya samu damar kai labari a zaben 2023, gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal ya ziyarci Ahmad Muhammad Makarfi har gidansa.