A iya nazarin da muka yi, mun fahimci cewa ba kome ba ne ya haifar da ita wannan matsalar ta rashin aikin yi ga matasa illa matsanancin dogaro da suka yi a kan aikin gwamnati.
Magance wannan matsala kuwa zai yiwu ne kawai idan aka samarwa matasan jari, domin yin kananan sana’oi wadanda suka dace da karkara, watau a turance cottage industry.
Saboda kuwa mu da muka kasance daliban tarihi, mun sani cewa wannan ita ce hanyar da manyan kasashen duniya masu arzikin masana’antu suka bi domin kaiwa ga wannan matsayin da suke a yau.
Matsalar rashin aikin yi musamman ga matasanmu wadanda suka kammala manyan makarantu, za mu iya cewa dai a yau abin ya yi kamari ta yadda ita kanta gwamnati ta rasa hanyar da za ta bi domin ganin an magance matsalar.
Su kuwa wadanda abin ya shafa, watau matasanmu masu takardun shaidar kammala babbar makaranta, kimarsu ta zube kasa warwas ta yadda a yau saboda matsalolin rayuwa, ta kai ga fagen kome kankantar albashi da wulakancin aiki karba suke idan aka basu.
Wannan kasida tamu ta yi la’akari ne da wadannan matsaloli na matasan tare da fahimtar cewa gwamnati ita kadai ba za ta iya magance wannan matsala ba.
Haka kuma ko shakka babu rashin samarwa matasanmu aikin yi, wanda ya dace da iliminsu babbar asara ce da kuma barazana ga zaman lafiya a jihohi da ma kasar baki daya.
Domin haka ne muka samar da wannan tsari namu mai suna KWALI JARI, wanda cikin yardar ALLAH muke fatar ya samar da mafita mai inganci da dorewa daga wannan matsala ta rashin aikin yi ga matasan.
Wannan suna kuwa na KWALI JARI shi muka ga ya fi dacewa da mu lakabawa mafitar. Abin nufi dai a nan shi ne za a nemi taimakon kananan hukumomi da masu hali a cikinmu domin su bayar da rancen kudade ga matasanmu da suka kammala manyan makarantu, a inda za a karbi kwalayin shaidar karatunsu a matsayin jingina.
Wannan tsarin namu gwamnatin tarayya ta yi amfani da shi sai dai kawai matasanmu na Arewa ba su amfana da tsarin ba kamar yadda ya kamata, saboda wasu sharudda masu 7 tsauri da gwamnatin tarayya ta gindaya na karbar rancen.
Dalilin haka ne muka ga ya fi dacewa mu fassara shi tsarin a cikin harshen Hausa, mu kuma sanya shi a cikin wannan kasidar tamu, saboda jawo hankalin gwamnatocinmu da masu halinmu su kawo dauki ga matasanmu domin ganin muma yankin namu ya amfana da tsarin kar mu kasance kamar kyandir a inda muka samar da mafita amma mu bamu amfana da ita ba sai wasu.
Babu tababa tsarin zai yi tasiri idan aka yi amfani da shi yadda ya dace a jihohi. Tsarin zai kuma taimaka sosai wajen raya karkara da yakar talauci, saboda kuwa dukkan wanda ya amfana da rance za a nemi ya yi sana’arsa a karamar hukumarsa ne ta asali.
Haka kuma tsarin zai karfafa guiwar wadanda suka amfana da rancen su yi hadin guiwa domin su samarwa kansu jari mai kwari da zai wadacesu yin sana’ar karkara (cottage industry) da shi.
Ya kamata mu karfafa guiwar matasan namu domin yin sana’a, wadda kuwa ita ce kawai hanya ma fi sauki a yanzu da za mu bi domin ganin mun amfana da iliminsu da kuma yawansu wajen gina al’umma.
Matasa dai kamar yadda kowa ya sani sune zuciyar kowace al’umma, wannan na nufin cewa, zaman lafiyarmu yana nan ga zaman lafiyar matasan namu.
Samun zaman lafiyar matasan kuwa yana nan ga ilimantar da su, da kuma samar masu abin yi, wanda zai dauke hankalinsu. Akwai kyakkyawar matashiya a garemu daga wata magana da tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahin Shekarau, ya yi, a inda ya ce matasa kamar ruwa suke; kodai a yi masu hanya ko kuwa su yi wa kansu hanya. Kiranmu dai a nan shi ne, mu yi wa ruwan hanya, kar mu bari ya yiwa kansa, domin kuwa yin hakan ba zai haifar mana da da mai ido ba….
Muna so a lura cewa, jihohinmu sun dade suna yin asara mai yawa, saboda rashin ingantattun dabaru na bayar da rance ga mabukata, da kuma gazawarsu na yin kyakkyawan amfani da dubban matasa, masu jini a jika, wadanda suka kammala karatunsu a manyan makarantu.
Har wayau, saboda yawan wadannan matasa, mu sani, ko jarin yin noma aka samar masu yawansu ya isa su ciyar da jihohinmu.
Gaskiyar magana dai ita ce, a yau babu wata kasa a wannan duniya tamu da za ta bunkasa idan har ta rasa yin kyakkyawan amfani da matasanta. Shin, ta wace hanya mu ‘yan Arewa za mu fita daga wannan kangin da muke ciki na rayuwa da talauci, bayan kuwa matasanmu ba su da aikin yi, har ma idan suna da shi, aikin nasu ba wanda zai taimaka wajen gina kasa ba ne, sai ma ya kashe kasa?
Muna da tabbaci cewa, saboda yawan wadannan matasa, da kuma ilimin da suke da shi, har idan aka samar masu da jari, domin yin sana’a, yankinmu da kasa baki daya za su share hanya ta ci gaba. Fa’idar Tsarinmu Ga Gwamnatin Jiha Fa’idojin da za a samu idan aka yi aiki da shawarwarin namu, ba ga matasan kawai za su tsaya ba, domin kuwa su kansu gwamnatocinmu, da al’ummominmu, akwai fa’idoji masu tarin yawa da za su samu.
Mun tsakuro muku wannan ne daga kasidar Dakta Aliyu M. Kurfi mai taken “Kwali Jari”