Ralf Rangnick ya ce dole a ga laifin tsohon kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer idan har kungiyar ta gaza kammala gasar Firimiyar Ingila a cikin kungiyoyi 4 na farko ko sahun gaba.
ya ce lallai akwai matsala, kuma zai yi wuya kungiyar ta samu gurbin zuwa gasar Turai, amma fa ya zake cewa Solskjaer, wanda aka sallama a watan Nuwamba zai kasance da laifi, duba da cewa ya jera rashin nasara 5 kafin a sallame shi.
A wasan da United ta buga da Southampton, sai da ta shiga gaba, amma aka farke, kuma hakan na faruwa ne a karo na 3 a jere, haka ma a wasansu da Aston villa ma, sai da suka saka kwallaye 2 kafin a farke.
Rangnick ya caccaki yadda ‘yan wasan suka murza tamaula bayan hutu a wasansu da Burnley, inda ya ce yana kokarin kawo karshen matsalar.
A wani labarin na daban Ralf Rangnick ya jinjina wa ‘yan wasan Manchester United da irin kokarin da suka yi, bayan da ya fara wasansa na farko da da kafar dama, inda suka lallasa Crystal Palace 1-0.
‘Yan wasan United sun bai wa sabon kocin tukuicin wasa cikin karkasashi, kana magoya bayan sun nuna goyon baya a gare shi ta wajen jinjina.
Duk da cewa ‘yan United sun samu nakasu a wasa bayan hutun rabin lokaci, dan wasan nan dan kasar Brazil Fred, ya saka kwallo daya tilo na wasan.
Wannan ne karon farko da Manchester United ta yi wasa ba tare da an saka mata kwallo a raga ba a gida, bayan jerin wsanni marasa armashi a ‘yan makonnin baya a karkashin tsohon koci Ole Gunnar Solskjaer, wanda kungiyar ta sallama a makon da ya gabata.