Wakilan kungiyar sun shaidawa jaridar Guardian cewa “Mambobin za su shirya wani yajin cin abinci na kwana daya a ranar Alhamis, domin mayar da martani ga yadda Isra’ila ke amfani da yunwa a matsayin makamin yaki ta hanyar hana abinci shiga zirin Gaza”.
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) – Abna ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar “Guardian” ta kasar Britania inda ta bayyana cewa, a ranar alhamis da dama daga cikin ma’aikatan gwamnatin Amurka za su shiga yajin cin abinci domin sukar manufofin shugaba Joe Biden na tallafawa yahudawan sahayoniya da kuma jawo hankali kan matsalar jin kai a zirin Gaza.
Kuma kungiyar da ke kiran kanta “الفدراليون المتحدون من أجل السلام” ta kunshi ma’aikatan gwamnati da dama.
Wakilan kungiyar sun shaidawa jaridar Guardian cewa “Mambobin za su shirya wani yajin cin abinci na kwana daya a ranar Alhamis, domin nuna adawa da yadda Isra’ila ke amfani da yunwa a matsayin makamin yaki ta hanyar hana abinci shiga zirin Gaza.”
Ana sa ran ma’aikatan gwamnatin tarayya da ke shiga yajin aikin za su zo ofisoshinsu su sanya bakaken kaya, ko sanya kufia ko wasu alamomin hadin kan Falasdinu.
Wanda yajin aikin da kungiyar ta shirya ta gudanar – a farkon wannan wata – ya samu mayar da martani mai karfi a birnin Washington, inda jami’an tsaron kasa na jam’iyyun biyu (Republican da Democratic) suka soki zanga-zangarsu tare da bayyana su a matsayin ‘yan tawaye.
Yajin aikin na nuni da yadda jami’an Amurka ke kara fusata, sakamakon kin amincewa da gwamnatin Biden ta yi na a gaggauta dakatar da bude wuta a Gaza, yayin da Isra’ila ta kai harin da ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da dubu 26, tare da jikkata wasu da dama fiye da dubu 65, da kuma gudun hijirar Falasdinawa kimanin miliyan 1.9.
Kuma ra’ayoyi mabambanta sun bayyana a cikin gida na manufofin gwamnatin ga ra’ayin jama’a a lokacin da Amurka ta fara kara yawan aika makamai da kayayyaki zuwa ga sahyoniyawan da suke kwacewa domin yin amfani da su a yakin Gaza.
Source: ABNAHAUSA