Shugaban Turkiyya Erdogan na fatan sasanta Rasha da Ukraine.
A karon farko tun bayan mamayar da Rasha ta ke yi wa Ukraine ta fara, ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun amince su gana a Turkiyya gobe Alhamis.
Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce yaa fatan tataunawar da za a yi a wani wurin hutu da ke kudancin kasarsa mai suna Antalya zai “bude kofofin da za su samar da yanayin tsagaita wuta na dindindin.”
Turkiyya na cikin kasashen kungiyar tsaro ta Nato amma ta yi kokarin fitar da wata matsaya da ta yi hannun riga da ta sauran kasashen yammacin Turai kan mamayar ta Rasha.
Duk da yace Turkiyya ba ta goyon bayan mamayar da Rasha ke yi, amma ya ce takunkuman da ake saka ma ta sun zama tamkar na “cin fuska da na ramuwar gayya kan al’ummar Rasha.”