A Mali,akalla mutane biyar da suka hada da jami’an Kwastam ne suka mutu bayan wani harin ta’addanci da aka kai a wani shiggen jami’an tsaro dake Koutiala na kasar Mali.
Rahotanni daga rundunnar tsaron kasar Mali na nuni cewa,nan take jami’an tsaron kasar ta Mali suka mayar da martani tareda kashe mahara da dama.
Majalisar sojin kasar Mali na iya kokari na ganin ta kawo karshen kungiyoyi dake dauke da makamai a arewacin kasar,al’amarin da ya sanya ta kulla yarjejeniyoyi da kamfanin Wagner na kasar Rasha da zai taimaka ta fuskar tsaro tare da bayar da horo ga jami’an tsaron kasar ta Mali tun bayan ficewar dakarun Faransa.
Tun a shekara ta 2012 ne kasar ta Mali ta fuskanci barrazanar mayaka masu ikirarin jihadi a karkashin inuwar Al-Qaida da Isil,al’amarin da ya hadassa rasa rayyukan farraren hula da dama a kasar ta Mali.
A wani labarin na daban kuma gwamnatin sojin Mali, ta sanar da kafa wata hukumar da za ta tsara sabon kundin tsarin mulki, bayan tsawaita wa’adin mulkin soja har zuwa shekara ta 2024.
Sanarwar da shugaban kasar Asimi Goita ya fitar da yammacin Jumma’a, ta nuna cewa hukumar za ta samu watanni biyu kafin ta kammala aikin ta.
Sanarwar ta ce hukumar za ta kunshi shugaban kasa, da wakilai biyu da masana kuma za ta tuntubi jam’iyyun siyasa, kungiyoyin farar hula, da masu dauke da makamai wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati, da shugabannin addinai da na gargajiya da kuma kungiyoyin kwadago.
A ranar Litinin ne shugaban mulkin sojan kasar Kanar Assimi Goita ya rattaba hannu kan wata doka da ta ce sojoji za su tafiyar da mulkin kasar har zuwa watan Maris din shekarar 2024, lokacin da za a gudanar da zabe.
Matakin ya dakile yunkurin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ke yi na gaggauta mika mulki ga fararen hula.