Liverpool ta shigar da bukatarta a hukumance, tana neman a dage karawa tsakaninta da Arsenal a gasar cin kofin Carabao a gobe Alhamis, matakin wasan gab da na karshe kuma zagaye na farko.
Kocin Liverpool Jurgen Kloop ya rasa damar halartar wasan da ‘yaransa suka yi a ranar Lahadin da ta gabata saboda gwaji ya nuna cewa, yana dauke da kwayar cutar.
Kazalika ‘yan wasa irinsu Allison da Joel Matip da Roberto Firmino dukkaninsu sun rasa halartar wasan na ranar Lahadin sakakamakon kamuwa da Koronar.
Baya ga matsalar Korona, Liverpool na kewar Moh. Salah da Sadio Mane da Nabty Keita da tuni suka koma kasashensu domin wakiltar su a gasar cin kofin Afrika da za a fara daga ranar 9 na wannan wata na Janairu a kasar Kamaru.
Yanzu haka, mahukuntan gasar firimyar Ingila sun ce, za su nazarci bukatar da Liverpool ta gabatar musu.
A wani labarin na daban Lauyoyin gwamnati sun shigar da karar masu horas da tawagogin kwallon kafa guda uku a Gabon bisa tuhumarsu da laifin yi cin zarafin kananan yara ciki har da yi musu fyade.
Tuhume-tuhumen na zuwa ne bayan wani sakamakon bincike da kafafen yada labarai suka wallafa kan zargin cin zarafin mata a farkon wannan watan, wanda shugaban Gabon Ali Bongo Ondimba ya kira lamari tsanani wanda kuma ba za a amince da shi ba, tare da ba da umarnin gudanar da bincike a dukkanin kungiyoyin wasanni na kasar.
A halin yanzu dai tsohon kocin kungiyar kwallon kafar Gabon ta ‘yan kasa da shekaru 17, Patrick Assoumou Eyi, tare da Orphee Mickala da Triphel Mabicka, suna fuskantar hukuncin dauri na shekaru 30 a gidan Yari idan har aka tabbatar da zargin da ake musu na yi wa mata fyade da yunkurin yi wa wata karamar yarinya fyaden.
Dan sanda mai shigar da kara Andre Patrick Roponat ya ce an mika mutanen uku zuwa ofishin mai gabatar da kara, kafin gurfanar da su gaban Kuliya manta sabo.
Wannan badakala dai ta kuma dabaibaye wani kocin wasan ‘yan taekwondo, Martin Avera, wanda aka kama shi da laifin lalata da yara tun a shekarun 1990.