Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kira babban darasin guguwar Aqsa ta koyar da samun nasarar wasu tsiraru masu karancin kayayyaki da kayan aiki suka samu amma tare da imani da azama yana mai cewa: Wannan gungu mai imani ya sami damar tarwatsa sakamakon kokarin da Yahudawa masu aikata laifuka na shekaru da dama da suka gabata ya watsa shi cikin iska a cikin ‘yan sa’o’i kadan.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: Jagoran juyin juya halin Musuluncin a wata ganawa da yayi da dubban dalibai a safiyar jiya, kan nazarin hanyar gano tushen kiyayyar da Amurka ta dade tana yi da al’ummar Iran, wanda ya kira ta’addancin da yahudawan sahyoniya da Amurka a Gaza da cewa abu ne wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihi da kuma ishara da irin farmakin kaskanci da juriyar tsayin daka na al’ummar Gaza yi haifar kan gwamnatin ‘yan ta’adda ta bogi da masu goyon bayanta masu girman kai, ya ce: Idan da babu cikakken taimako daga Amurka ga gwamnatin Sahayoniya da ta gurgunce nan da ‘yan kwanaki. Haka nan kuma ya kamata al’ummar musulmi su tashi tsaye wajen yakar wannan gwamnati ta hanyar katse hadin gwiwar tattalin arziki da gwamnatin sahyoniyawan da kuma aiwatar da muhimman ayyukan da suke da shi a wannan arangamar da ke tsakanin fagen gaskiya da fagen karya ta hanyar dagewa kan dena jefa bama-bamai da aikata laifuka a Gaza nan take”.
Ayatullah Khamenei kuma yayin da yake ishara da yadda yahudawan sahyuniya suka dogara da taimakon Amurka, ya kara da cewa: Idan ba don goyon bayan Amurka da taimakon makamanta ba, da a cikin makon farko ne gwamnatin sahyoniyar cin hanci da rashawa da karya da kama karya ta rushe , don haka musibar da yahudawan sahyoniya suka saukar a Gaza a yau tana dogare ne da taimako bisa hakikanin gaskiya a Hannun Amurkawa ne.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira kisan da aka yi wa yara 4,000 a cikin makonni uku a matsayin laifi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi, tare da jaddada taka tsan-tsan da al’ummar musulmi suke yi dangane da abubuwan da suke faruwa a zirin Gaza, wanda a hakikanin gaskiya fagen rikici ne tsakanin gaskiya da karya da kuma imani da girman kai, inda ya ce: “Ikon girman kai tare da Bama-bamai, matsin lamba na soja, bala’o’i da laifuffuka suna faruwa, amma ikon bangaskiya da imani ya iya shawo kan waɗannan duka da taimakon Allah.
Yayin da yake bayyana nasarorin da juriya da jajircewar al’ummar Gaza suka samu, ya ce: Zukatanmu sun cika da jini saboda irin wahalhalun da al’ummar Palastinu ke ciki musamman Gaza, amma idan aka yi la’akari da abin da ke faruwa a fili yake cewa wadanda suka yi nasara na wannan filin su ne mutanen Gaza da Palastinu, waɗanda suka iya yin manyan ayyuka.
Ayatullah Khamenei ya yi la’akari da yaye da rufin fuskar karya na kare hakkin bil’adama daga fuskokin turawan yamma da kuma tozartasu daga sakamakon juriya da tsayin daka na al’ummar Gaza ne kuma ya kara da cewa: Al’ummar Gaza sun motsa lamirin bil’adama da juriyarsu Kun ga a yau, hatta a titunan Amurka da kasashen Yamma, jama’a da dama suna rera taken nuna adawa da Isra’ila, a lokuta da dama na nuna adawa da Amurka.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira kalaman wasu majiyoyin yammacin duniya, kamar kungiyoyin da ke goyon bayan Falasdinu a Ingila da Iran ta yi, ya haifar da sakamakon rashin jin dadinsu da ba za su iya warkewa da, ya kuma ce yana mai yin kinaya fa wadannan bayanai na ban dariya da cewa: Ba makawa wadannan taruka aikin shiryarsu ya samu ne daga Ƙungiyar Landan da Paris!
Da yake ishara da abin kunya na makaryata na duniya, ya kira kiran da a kaiwa mayakan Falasdinawa da ‘yan ta’adda a matsayin wata alama ta hakikanin rashin kunyar ‘yan siyasa da kafafen yada labarai na yammacin Turai, ya kuma yi tambaya: Shin wanda yake kare gidansa da kasarsa dan ta’adda ne? Shin Faransawan da suka yaki Jamusawa a Paris a yakin duniya na biyu ‘yan ta’adda ne? Ta yaya suka kasance mayaka kuma abin alfahari ga Faransa, amma matasan Jihad da Hamas suka zamo ‘yan ta’adda?
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kira babban darasin guguwar Aqsa da cewa nasarar wasu tsiraru masu karancin kayayyaki da shiri suka samu amma tare da imani da azama yana mai cewa: Wannan kungiya mai imani ta samu damar bice sakamakon yunkurin aikata laifuka na shekaru da dama da suka gabata na abokan gaba kuma bice shi yabi iska a cikin ‘yan sa’o’i kadan.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kara da cewa: Haka nan kuma Palasdinawa sun kaskantar da gwamnatin mamaya da gwamnatocin ma’abuta girman kai da suke goyon bayanta ta hanyar ayyukansu da jarumtarsu wanda a yau da hakurin da suke da shi suka samar da shi.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da jiran tsammanin mai ribanye da kasashen musulmi suke yi a kan laifuffukan gwamnatin mamaya, ya ce: Idan a yau gwamnatocin Musulunci ba su taimaka wa Palastinu ba, to kuwa sun karfafa makiya Palastinu, wanda a hakikanin gaskiya su makiyi Musulunci ne da bil’adama, sannan kuma ya ce; wannan Hatsarin dai shi zai yi musu barazana a nan gaba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada wajabcin hada kan al’ummar musulmi, inda ya kira dagewar da gwamnatocin kasashen musulmi suka yi na gaggauta dakatar da ayyukan ta’addanci da hare-haren bama-bamai a zirin Gaza, inda ya kuma bukaci wadannan gwamnatocin da su hana fitar da man fetur da abinci zuwa ga gwamnatin sahyoniyawan kuma kar suyi da hadaka ta fuskar tattalin arziki ba. kamata ya yi gwamnatoci da kuma a dukkan majalisu na kasa da kasa, su yi Allah wadai da laifuffuka da bala’o’in gwamnatin ‘yan ta’adda a fili, ba tare da dar-dar ba, ko kuma yin magana biyu.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayin da yake jaddada rashin mamadi na irin barnar da aka yi wa gwamnatin Sahayoniyya da kuma jami’an gwamnatin ‘yan mamaya Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Gwamnatin mamaya tana da matukar koma baya da rudani ta yadda ta yi karya ga al’ummarta, kamar su nuna damuwa game da fursunonin ta da ya zama karya ne domin fursunonin za su iya halaka sakamakon jefa bama-bamai da su ke yi.
Ayatullah Khamenei ya yi kira ga al’ummar musulmi da su kula da cewa, wanda ke adawa da Musulunci da kuma al’ummar Palastinu da ake zalunta ba wai gwamnatin sahyoniya ce kadai ba, har ma da Amurka da Faransa da Ingila, kuma bai kamata musulmi su kar su manta tattauna wannan hakikar abunda ke faruwa a cikin lamuririnsu da cikin kulla alaka da nazarorinsu ba.
Yayin da yake ishara bisa dogaro da ayar kur’ani mai girma da ke cewa: “Tabbas Alkawarin Allah gaskiya ne, wadanda kuma ba su yi imani da shi ba, kar su girgiza ku su raunanaku” ya jaddada cewa: In sha Allahu nasara ba tare nisa ba tana ga Falasdinu da mutanenta.
A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei, yayin da yake ishara da waki’oi uku a ranar 13 ga watan Aban, ya ce: Amurkawa sun hari al’ummar Iran sau biyu; A ranar 13 ga Aban 1343, bayan shelantawar Imam Khumaini mai tsanani da ke adawa da kudurin “fifikon Amurkawa a Iran na sama da shari’a kan kowane laifi”, hakan yasa suka yi masa hijira kuma ranar 13 ga Aban 1957, a zamanin da hukumar Iran ‘Yar koran amurke wani Ya kashe wasu dalibai a gaban jami’ar Tehran.
Ya kara da cewa: Amma a wakia ta uku, wato kame ofishin jakadancin Amurka da dalibai suka yi, al’ummar Iran sun kai wa Amurka hari tare da tona asirin da kuma boye bayanan ofishin, lamarin da ya lalata martabar Amurka a duniya.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kuma kara da cewa bai kamata matasa su takaita da harkokin motsa zuciya ba da kokarin fahimta da nazari kan batutuwa daban-daban ba, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Wajibi ne a samar da ingantaccen nazari da kimanta manufofin juyin juya halin Musulunci, kariya mai alfarma, batutuwa daban-daban na juyin juya halin Musulunci na kwanakin gomomi na 60s, da bambancin kwanaki gomomi na shekarun 70s, da al’amura daban-daban na kwanakin 80s da 90s…
Source: ABNAHAUSA