Hezbollah ta kara da cewa harin nata martani ne ga kisan da Isra’ila ta yi wa fararen-hula ‘yan kasar Lebanon kwanakin baya.
0840 GMT —Wani Ministan Isra’ila ya ce suna da ‘zabin’ yin amfani da ‘bama-baman nukiliya’ a Gaza
Ministan Al’adun Isra’ila Amichai Eliyahu ya ce akwai yiwuwar su yi amfani da ‘bama-baman nukiliya’ a Gaza, kamar yadda kafafen watsa labarai na kasar suka rawaito ranar Lahadi.
Eliyahu, minista na jam’iyya Otzma Yehudit mai tsattsauran ra’ayi, ya ce “daya daga cikin zabin da muke da shi a yakin shi ne mu jefa bama-baman nukiliya a Zirin Gaza,” in ji jaridar Times of Israel.
A yayin da ake hira da shi a wani gidan rediyo, Eliyahu ya nuna “adawa kan bari a shigar da kayan agaji Gaza.”
0157 GMT — An kashe sojojin Isra’ila 345 tun daga 7 ga watan Oktoba
Rundunar sojin Isra’ila ta ce dakarunta 345 ne suka mutu tun da ta soma kai hare-hare a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba.
Kakakin rundunar sojin Daniel Hagari ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gudanar ranar Asabar, bayan an kashe karin sojinsu hudu a Gaza.
Ya kara da cewa an kashe sojojin Isra’ila 29 tun daga ranar Talata lokacin da suka kaddamar da hari ta kasa a Gaza.
Hagari ya ce za su ci gaba da yaki a dukkan sassaan Gaza har sai sun wargaza kungiyar Hamas ta Falasdinawa.
Hagari ya kara da cewa an kashe sojojin Isra’ila 29 tun daga ranar Talata lokacin da suka kaddamar da hari ta kasa a Gaza.
0100 GMT — Hezbollah ta ce ta kashe sojojin Isra’ila a arewacin kasar
Kungiyar Hezbollah ta ce ta kai hari kan sojojin Isra’ila da dama a cikin wani gida a matsugunin Metula da ke arewacin Isra’ila.
Kungiyar da ke Lebanon ta ce ta kashe sojojin Isra’ila da dama a harin.
Ta kara da cewa harin nata martani ne ga kisan da Isra’ila ta yi wa fararen-hula ‘yan kasar Lebanon kwanakin baya.
Rundunar sojin Isra’ila ta yi ikirarin cewa babu wani sojanta da aka jikkata a harin da Hezbollah ta kai sannan ta ce jiragen yakinta sun kai hare-hare da dama a yankunan Hezbollah da ke kudancin Lebanon.
2300 GMT — Isra’ila ta kashe Falasdinawa 51, ta jikkata gommai a sansanin ‘yan gudun hijira na Gaza — Faladinu
Isra’ila ta kashe Falasdinawa akalla 51 sannan ta jikkata gommai a harin da ta kai ta sama a sansanin ‘yan gudun hijira na Al Maghazi da ke tsakiyar Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na Falasdinawa WAFA.
Kakakin Ma’aikatar Lafiya ta Gaza, Ashraf al-Qidra, ya ce an kashe mutane da dama ba tare da ya bayar da hakikanin alkaluman wadanda suka mutu ba, sai dai ya kara da cewa gommai sun jikkata kuma suna kwance a dandarin kasa a sashen bayar da agajin gaggawa na asibiti.
Maghazi yana yankin Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza.
Ganau sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa hare-haren sun fada kan gidaje da dama.
“Isra’ila ta kai hari ta sama a gidajen makwabtana da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Maghazi, an lalata tagogin gidan da ke kusa da nawa,” in ji Mohammed Alaloul, mai shekara 37, wani dan jarida da ke aiki da kamfanin dillancin labarai na Anadolu na Turkiyya.
Alaloul ya shaida wa AFP cewa harin ya yi sanadin mutuwar ‘ya’yansa Ahmed, dan shekara 13 da kuma Qais, dan shekara hudu, tare da dan uwansa. An jikkata mahaifiyarsa da matarsa da kuma wasu ‘ya’yansa biyu.
Source: TRT AFRICA