Kungiyar Tarayyar Turai (EU) na tattaunawar gaggawa game da yiwuwar sake laftawa Rasha wasu takunkumai, bayan jerin hare-hare da dakarun kasar suka kai, da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane a sassan Ukraine.
A cewar sa, Tarayyar Turai (EU) na goyon bayan Ukraine, kuma ba zata zuba wa Rasha ido ta ci gaba da kisan kare dangi a kasar ba.
Ko da yake jawabi guda daga cikin manyan jagororin kungiyar, ana ci gaba da tattaunawa kan irin takunkumin da za’a sanyawa Rasha a wannan karon don kuwa ya zama wajibi a sanya wanda zata ji a jikin ta.
Tarayyar Turai ta kuma ce abin takaici ne irin kisan fararen hula da dakarun Rasha suka yi a garin Bucha, inda aka sami gawarwakin mutane da dama, abin da ta kira da yunkurin kisan kare dangi.
Daga nan kuma sai kungiyar ta bukaci babban mai shigar da kara na Ukraine da ya mayar da hankali a wajen tattara hujojjin kisan fararen hula, wadanda za’a yi tawassali da su a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, bayan gurfanar da Rasha.