Kotun daukaka kara a kasar Rwanda ta amince da hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari da aka yi wa tauraron fim din Hotel Rwanda, wato Paul Rusesabagina wanda aka samu da laifin ayyukan ta’addanci bara.
Regis ya ce, tun da Rusesabagina bai taba aikata wani laifi ba sai a wannan karon, kotun ba za ta amince da bukatar kara masa shekaru ba, saboda haka ta amince da hukuncin daurin shekaru 25 da aka masa bara.
Rusesabagina mai shekaru 67 wanda ya ki zuwa zaman kotun baki daya, yau ma ya kauracewa zuwa yanke hukuncin.
Ana danganta shi da ceto rayukan mutane sama da 1,200 lokacin kisan kiyahsin da aka yi a shekarar 1994 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 800,000 akasarinsu ‘Yan Kabilar Tutsi.
A wani labarin na daban kuma Tsohon Gwamnan Jihar kano dake jamhuriyar Najeriya Rabiu Musa Kwankwaso ya kawo karshen zamansa a cikin Jam’iyyar PDP sakamakon sanarwar da yayi na ficewa daga cikin ta.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce sakamakon wasu dalilai na rashin fahimtar juna, ya yanke hukuncin ficewa daga jam’iyyar daga yau Talata, 29 ga watan Maris na shekarar 2022.
Kafin dai wannan lokaci an dade ana rade radin cewar injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso zai sauya sheka zuwa Jam’iyyar NNPP domin tsayawa takarar zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Tuni wasu daga cikin magoya bayan sa suka fice daga PDP domin komawa sabuwar Jam’iyyar a Jihar Kano da kuma wasu jihohi dake cikin fadin kasar.