Gwamnatin Burkina Faso ta ce kungiyar raya Tattalin Arzikin kasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta aike da tan dubu 10 na kayan abinci ga kasar.
Ministar harkokin wajen kasar Olivia Rouamba ta tabbatar da karbar tallafin a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis.
A cikin watan Janairu, ECOWAS ta dakatar da gwamnatin da ke mulkin sojan Burkina Faso, biyo bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaba Roch Marc Christien Kabore da sojojin suka yi, a karkashin jagorancin Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba.
A ranar Litinin da ta gabata, gwamnatin sojin Burkina Faso ta ki amincewa da bukatar ECOWAS na neman rage wa’adin shekaru uku da ta dibarwa kanta kafin sake mikawa farar hula mulki.
A wani labarin na daban kuma Daya daga cikin wadanda ke neman ja’iyyar PDP ta tsayar dasu takarar neman kujerar shugabancin Najeriya a zaben 2023, kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya ce zai nada minista mai kula da cika ciki, wanda zai tabbatar da kowa ya koshi idan ya zama shugaban Najeriya.
Fayose ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, jim kadan bayan bayyanar sa a gaban kwamitin tantance masu neman Jam’iyyar PDP ta tsayar da su takarar shugaban kasa, a ranar Juma’a.
Tsohon gwamnan ya ce a lokacin da kwamitin ya tambaye shi manufofinsa kan samar da ababen more rayuwa domin hana yunwa a lokacin da yake gwamnan jihar Ekiti, ya bayyana karara cewa zai maimaita hakan idan ya zama shugaban kasa.
Gwamnan ya ce, samawa mutane ababen more rayuwa kamar tituna masu kyau da dangoginsu na da muhimmanci, sai dai fa hakan ba zai wadatar ba, idan har jama’a na fama da yunwa.
A ranar Juma’ar da ta gabata babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta kori biyu daga cikin ’yan takara 17 da ke neman ta tsayar da su a zaben shugaban kasa.
Shugaban kwamitin tantance ‘yan takarar Sanata David Mark ne ya bayyana daukar matakin yayin ganawa da manema labarai, jim kadan bayan kammala aikin da suka yi a birnin Abuja.
Sai dai Sanata Mark, ya ki bayyana sunayen wadanda aka hana su takara ko kuma dalilan da suka sanya aka soke su, illa kawai bayanin da yayi na cewa ba su cika sharudan da ake bukata ba.