Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana goyan bayan kungiyar kasashen Afirka ta AU wajen jagorancin sassanta rikicin kasar Libya, bayan ya amince da watsi da kungiyar da kasashen duniya suka yi wajen sasanta rikicin.
Guterres dake halartar taron kungiyar kasashen Afirka dake gudana a Addis Ababa yace ya fahimci fushin kungiyar, kuma ya zama wajibi a sanya ta cikin duk wani yunkuri.
Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa da zai karbi shugabancin kungiyar AU daga ranar litinin yace shugabancin sa zai mayar da hankali kan warware rikicin kasar Libya.
Shugabannin kungiyar kasashen Afirka sun koka kan yadda aka sanya su a gefe, a yunkurin da kasashen Duniya keyi wajen sassanta bangarorin dake rikici a Libya, cikin su harda Majalisar Dinkin Duniya da wasu kasashen Turai.
Kasar Libya ta fada cikin tashin hankali tun daga shekarar 2011 lokacin da kungiyar NATO ta goyi bayan boren da ya kawar da shugaba Muammar Ghadafi daga karagar mulki.
Yanzu haka kasar a rabe take tsakanin gwamnatin dake samun goyan bayan Majalisar Dinkin Duniya da shugaban Yan Tawaye Janar Khalifa Haftar.
A wani labarin na daban Jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun tsare ministan sadarwar kasar Mahamadou Zada inda ake tuhumarsa da almubazzaranci da kudaden talakawa lokacin da ya jagoranci wata hukumar gwamnati.
Kamfanin dillancin labaran Faransa yace ma’aikatan shari’a ta yiwa Zada tambayoyi dangane da zargin da ake masa na bacewar kudin da ya kai kusan Dala miliyan 6 daga hukumar dake kula da ayyukan hakar ma’adinai wanda ya jagoranta tsakanin shekarar 2013 zuwa shekarar 2021.
Kafofin yada labaran Nijar sun ce a shekarar da ta gabata aka bankado bacewar kudaden, abinda ya sa kaddamar da bincike akan lamarin.
Kafofin yada labaran cikin gidan Nijar sun ce wannan badakala ta samo asali ne a shekarar da ta gabata, lokacin da kamfanin Taanadi, da yayi fice wajen bayar da lamuni, ya ce ya kasa gano CFA biliyan uku da kamfanin Sopamin ya ce an aika cikin asusunsa.
Shekaru goma da suka gabata, kamfanin Sopamin ya shiga cikin wata badakala da ta shafi cinikin Uranium na kasa da kasa da Kamfanin Areva ta Faransa ya shirya wanda a yanzu aka sauya masa suna zuwa Orano.