Pierre Emerick-Aubameyang ya ci kwallo 3 rigis a wasan da aka fara da shi a Barcelona, a wata fafatawar da suka yi wa Valencia ci 4-1 a gasar La Ligar Spain, lamarin da ya kai Barcelonar cikin jerin kungiyoyi 4 na farkon teburin gasar.
A ganawarsa da manema labarai bayan wasan, Aubameyan ya ce abokin wasansa Pedri ne ya ci kwallonsu ta 4, amma daga bisani Barcelona ta tabbatar da cewa alkalin wasa ya bai wa Aubameyan kwallon, lamarin da ya bai wa dan wasan gaban na kasar Gabo ,kwallayensa 3 rigis a wasa guda.
Wannan ne karo na farko da aka fara wasa da dan wasana a gasar Laliga tun da ya Arsenal ta soke kwantiraqginsa a watan da ya gabata.
Pierre-Emerick Aubameyang zai ci gaba da kasancewa dan wasan Arsenal, a cewar kocin kungiyar, Mikel Arteta.
Dan wasan mai shekaru 32 ya ci kwallaye 3 rigis a wasan neman cin kofin Carabao da Arsenal ta lallasa West Brom da ke wasa a gasa ta kasa da Firimiya 6-0 a daren Laraba, kuma ita ce nasarar kungiyar ta farko a wannan kaka, bayan rashin nasara 2 da ta samu a gasar lig.
A wani taron manema labarai, a Alhamis din nan, Arteta ya ce aubameyanga dan wasan Arsenal ne, kuma zai ci gaba da kasancewa a kungiyar.