Akalla mutane milyan 25 ne aka tanttance za su kada kuri a zaben yan majalisun dokkokin kasar Iraqi a yau Lahadi. Iraqi,kasar da tattalin arzikinta ya durkushe da kashi 11, yayin da a gefe guda Asusun bada Lamuni na duniya IMF ya ce akalla kashi 40 na yawan al’ummar kasar da ya kai miliyan 40 na cikin kangin talauci.
A hukumance a shekara ta 2022 ne ya dace a gudanar da wannan zabe,don kawo karshen boren jama’a dake zargin gwamnati da gazawa, a shekara ta 2019,yayi zanga-zangar da ta gudana akalla mutane 600 ne suka bakuci lahira,wasu dubu 30 suka samu rauni a wancan lokacin a kasar ta Iraqi.
A wani labarin na daba dubun dubatar masu zanga-zanga a Iraqi sun farmaki Ofishin jakadancin Amurka yau Talata bayan farmakin jiragen yakin Amurkan a karshen mako kan sansanin sojin da ke samun goyon bayan Iran a cikin kasar ta Iraqi da ya kashe akalla mayakn Hezbollah 25.
Yayin boren na yau dai masu zanga-zangar sun rika kona tutocin Amurka tare da furta kalamai masu zafi ga gwamnatin ta Amurka, matakin da ya tilasta girke jami’an tsaro da nufin tarwatsa su ta hanyar harba musu hayaki mai sanya hawaye da ruwan zafi.
Farmakin masu zanga-zangar na zuwa dai dai lokacin da gwamnatin Iraqi ke cewa ya zama wajibi ta yi nazari a game da alakar da ke tsakaninta da Amurka, bayan da jiragen yakin kasar ta Amurka suka kai farmaki kan sansanin mayakan da ke samun goyon bayan Iran a cikin kasar ta Iraki.
Sanarwar da gwamnatin kasar ta Iraki ta fitar, ta bayyana harin a matsayin wanda aka kai saboda dalilai na siyasa amma ba domin al’ummar Iraki ba, abin da ke nufin cewa ya zama wajibi a yi nazari tare da daukar mataki dangane da lamarin.
Sanarwar ta ce harin ba wani abu ba ne face keta hurumin Iraki a matsayinta na kasa mai cikakken ‘yanci sannan kuma ya yi hannun riga da manufofin rundunar kawance da kasashen duniya suka kafa don yaki da ayyukan ta’addanci a yankin.
Washe garin wannan hari da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 25 da raunata wasu 51, an samu barkewar zanga-zanga a cikin kasar ta Iraki, yayin da aka samu rahotannin kona tutar Amurka.
A martanin da ta fitar dangane da lamarin, ma’aikatar harkokin wajen Rusha, ta bayyana musayar wuta tsakanin Amurka da Hezbollah a matsayin abin asha, yayin da ita kuma Iran ta bayyana harin a matsayin wata alama da ke tabbatar wa duniya cewa Amurka na goya wa ta’addanci baya ne.