Hukumar yaki da shan haramtattun kwayoyin karin kuzari a wasannin motsa jiki ta duniya wato AIU, ta haramtawa fitacciyar ‘yar wasan motsa jiki ta Najeriya, Blessing Okagbare shiga wasanni har tsawon shekaru 10, bisa samunta da ha’inci wajen shan haramtattun kwayoyin.
‘Yar Najeriyar dai ta taba lashe lambar Azurfa a gasar Olympics ta shekarar 2008.
Okagbare ta tsinci kanta cikin halin tsaka mai wuya ne duk da cewar ba a bayyana sunanta cikin wata tuhuma da aka gabatar ba a Amurka cikin watan da ya gabata a kan wani likita mazaunin birnin Texas, Eric Lira, da ke samarwa ‘yar Najeriyar kwayoyin.
Jami’an ma’aikatar shari’ar Amurka a New York sun ce Eric Lira, mai shekaru 41 wanda ke zaune a El Paso, ya baiwa ‘yan wasa biyu magunguna karin kuzari da zummar taimaka musu wajen tafka magudi a yayin wasannin motsa jikin gasar Olympiics a Tokyo.
A wani labari na daban Kwamiti na musamman da ke sa`ido kan tabbatar da da`a na karkashin hukumar shirya wasannin motsa jiki ta duniya IAAF, ya ce haramcin da aka kafawa `yan wasan motsa jiki na kasar rasha zai ci gaba da kasancewa har zuwa watan Nuwamba na shekarar da muke ciki.
Tun a watan Nuwanban shekara ta 2015 aka haramtawa `yan wasan Rasha da dama shiga wasannin motsa jiki, bayan rahoton da Hukumar yaki da shan kwayoyin Karin kuzari WADA mai zaman kanta ta wallafa na zargin gwamnatin Rasha da goyon bayan `yan wasanta wajen shan kwayoyin.
A shekarar 2016 da ta gabata aka sake tabbatar da haramcin kan Rasha, wanda hakan yasa mafi yawancin `yan wasan Rasha suka gaza shiga gasar Olympics da ta gudana a birnin Rio na Brazil.