Amurka ta ce za tya aike da karin dakaru dubu 3 zuwa Poland don kara wa kawayenta na NATO kwarin gwiwa a daidai lokacin da fargabar Rasha za ta mamaye Ukraine ke ci gaba da karuwa.
Tun a karshen watan Janairu ne aka sanya dakarun na musammana a cikin shirin ko-ta-kwana, bayan da shugaba Joe Biden ya bukaci haka.
Wani babban jami’i a ma’aikatar tsaron Amurka ya ce dakarun za su bar sansaninsu a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, kuma za su sauka Poland ne a cikin mako mai zuwa.
Wadannan dakaru za su hade ne da 2000 da aka sanar da isarsu Poland a ranar 2 ga watan Fabrairu.
A wani labarin na daban Iraqi ta maido da ‘yan kasarta kusan dubu 4 da suka makale akan iyakokin Belarus da Poland da Lithuania da Latvia a ‘yan makwannin nan.
Mai Magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iraqi, Ahmed al-Sahaf ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, jumullar ‘yan gudun hijira dubu 3 da 817 aka yi nasarar maido da su gida daga Belarus, baya ga 112 da aka kwaso daga Lithuania.
Mista Sahaf ya ce, har yanzu akwai dimibin ‘yan Iraqi da ke ci gaba da makalewa a Belarus, sannan an gaza tantance ainihin adadinsu saboda matsalar yanayin muhallinsu.
Tun kakar da ta gabata ne, dubban ‘yan gudun hijira akasarinsu daga yankin gabas ta tsakiya musamman daga Iraqi, suka yada zango tare da kafa sansaninsu a kan iyakar Belarus da EU, yayin da suke fuskantar yanayi mai matukar wahala a fafutukarsu ta ratsawa cikin kasashen Turai.
Kasashen yammacin duniya sun zargi Belarus da kokarin bude wa ‘yan gudun hijirar kofar kwarara cikin kasashen Turai, a wani mataki na ramuwar gayya kan takunkuman da Turai ta kaka wa gwamnatin shugaba Alexander Lukashenko na Belarus.