Libiya Ta Sake Fadawa Rudani, Bayan Da Ta Tsinci Kanta Da Firaministoci Guda Biyu.
A Libiya a shiga wata sabuwar dambarwa bayan da kasar ta tsinci kanta da firaministoci guda biyu.
Hakan dai ya biyo bayan da majalisar yankin Tobrouk ta nada tsohon ministan cikin gida Fathi Bachagha, a mukamin, bayan cimma wata yarjejeniyar siyasa a tsakanin bangarori da dama na yankin cikin har da gungun masu dauke da makamai ciki har da dakarun dake biyaya ga Janar Khalifa Haftar.
A nasa bangare kuwa Abdel Hamid Dbeibah, wanda ke samun goyan bayan MDD, ya ce shi kam ba zai mika mulki bag a wata gwamnatin wacce ba’a zaba ba.
Tuni dai aka fara nuna damuwa game da makomar kasar bayan kasa shirya zabubukan da ake kallo masu mahimmanci a gare ta a watan Disamba da ya gabata.
Dama Libiya ta saba fadawa irin wannan dambarwar inda ko a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016 ta fuskanci shugabancin na gwamnatoci guda biyu.
A wannan Juma’ar babban sakataren MDD, Antonio Guterres, ya bukaci dukkan bangarorin dasu ci gaba da samar da yanayi na zaman lafiya a kasar da kuma sgirya zabubuka cikin lokacin da ya tsawaka.