Sudan; Shugaban Kasa Ya Bukaci ‘Yan Adawa Su Ajiye Bambance-Bambance Tsakaninsu Da Gwamnati.
Shugaban majalisar mulki ta kasar Sudan Abdulfattah Alburhan ya yi kira ga gamayyar jam’iyyun adawar kasar zuwa hadin kai da kuma ajiye dukkan bambamce-bambance da ke tsakaninsu don kafa gwamnati.
Tashar talabijin ta Aljazeera dake kasar Qatar ta nakalto Janar Burhan yana fadar haka a sakonsa na taya mutanen kasar murnar sallar Idi karama.
Har’ila yau labarin ya kara da cewa shugaban ya bayyana cewa a shirye yake ya hada kai da dukkan jam’iyyun siyasa wadanda suke son ci gaban kasar Sudan da kuma ganin cewa ta fita daga cikin matsalplom da ta fama da su a halin yanzu.
READ MORE : Kan Kasashen Turai Ya Rabu A Lokacinda Rasha Ta Rufe Fampon Isakar Gas Ga Wasu Kasashe.
A wani bangare kuma shugaban Burhan y ace dole ne a sauya wasu dokokin kasar saboda kawo karshen rikicin kabilanci wanda ya ki ci yaki cinyewa a wasu sassan kasar.
READ MORE : Siriya; An Yi Kokarin Kishe Shugaban Asad Ba Tare Da Samun Nasara ba.
READ MORE : Bikin Ranar Ma’aikata Ta Duniya, 02 May 2022.
READ MORE : Najeriya; Shugaban Buhari Ya Bayyana Cewa An Kusan Kawo Karshen ‘Yan Ta’adda A Kasar.