Hamas Ta Jinjinawa Jagora Kan Tallafin Da Take Samu Daga Kasar Iran.
Kakakin kungiyar Hamas wacce take gwagwarmayar kwatar kasar Falasdinu da aka mamaye ya mika godiya da kuma jinjinawa jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Khaminei dangane da irin tallafin da kungiyar da kuma al-ummar Falasdinu take samu daga kasar Iran a gagarumin jihadin da take yi da yahudawan Sahyoniyya.
Tashar talabijin ta Al-Mayadin ta kasar Lebanon ta nakalto Abu Ubaida kakakin rundunar izzuddin al-Kassam, reshen sojoji na kungiyar Hamas yana fadar haka ya kuma kara da cewa jajircewan da JMI tayi duk tare da matsalolin da take fama da su, tare da al-ummar Falasdinu abin yabone da kuma godiya musamman ga Imam sayyid Aliyul Khamina’i.
READ MORE : Sudan; Shugaban Kasa Ya Bukaci ‘Yan Adawa Su Ajiye Bambance-Bambance Tsakaninsu Da Gwamnati.
Kamfanin dillancin labaran Iran Press ko IP, har’ila yau ta nakalto Abu Ubaida yana cewa, dakarunsa suna mika godiya ta musamman har’ila yau ga Janar Husain Salami shugaban dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran dangane da goyon bayan da yake bawa gwagwarmayan al-ummar Falasdinu.
READ MORE : Kan Kasashen Turai Ya Rabu A Lokacinda Rasha Ta Rufe Fampon Isakar Gas Ga Wasu Kasashe.