Jarumi Mustapha Nabraska ya saki sabon bidiyo cike da bacin ai inda ya caccaki gwamnati kan watsi da jama’a da tayi ba tare da sauke hakkinta ba.
Mai bada shawara na musamman din ga Gwamna Ganduje, ya ce sune suka tallatawa jama’a Buhari, don haka dole su fadi gaskiya a yanzu.
A cewarsa, idan mahaifiya, kanwa, ko ‘dan uwan wani shugaba ne a hannun ‘yan ta’adda, ai ba zasu nuna halin ko in kula a kai ba Ya kara da cewa tabbas Allah ya la’anci shugaba mara adalci kuma za a yi musu hisabi daidai da yadda suka yi wa mutanensu saboda amana ce gare su.
Fitaccen jarumin masana’antar Kannywood kuma mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Mustapha Nabraska, ya caccaki gwamnatin Buhari.
A bidiyon da Naraska ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya yi kira ga gwamnati da tayi abinda ya dace idan ba haka ba zasu sake yi wa kowa kamfen ba.
A kalaman jarumin: “Yau idan mahaifiyarka ake duka, ya zaka ji a ran ka? Ko ‘dan ka, ko wanka ko wani naka na jini?
An kama mutane, babu wani abu, an yi shiru an kasa karbarsu, an kasa cewa komai a daidai lokacin da rayuwa tayi tsada, abincin da zaka sa a bakinka ya gagareka, baka da ruwan sha, baka da wuta, baka da isasshen tsaro wanda zai taimaka maka wurin gudanar da rayuwartaka.
“Ba a daji ake yin zabe ba, a garuruwa ko jihohi ake yin zabe kuma da kuri’ar al’umma ake kirgawa a ci zabe, ba ta aljanu ba.
Ba kuma daji ake kai akwati a yi zabe ba. Mun bada gudumawa, mun taimaka wurin tallata gwamnati tare da manufofinta.
Nabraska yace: “Mun taimaka wurin tallata ayyukan da gwamnatin take yi na zahiri da na badini. Don haka idan an yi ba daidai ba dole a fito a bayyana domin al’umma su san cewa ana shiga lamarinsu kuma ana jibantar lamarinsu.”
Cike da takaici ya kara da cewa: “Wannan abu hakki ne na ‘yan kasa, kuma a karbo su. Ku duba, an maida mata zawarawa, wasu an maida su marayu, wasu babu mata.
An shiga halin kunci. Mu dake cikin jama’a mun fi kowa sanin halin kunci da matsin rayuwa da ake ciki.
“Wallahi sai Allah tsinewa shugaba kuma yayi masa hisabi ranar kiyama daidai da yadda al’umma suka tsinta kansu a ciki. Mutum ya bar ganin yana cikin tsaro, baka cikin tsaro matukar baka shiga lamarin al’umma ba.
Baka cikin tsaro idan baka tsare dukiya da rayukan al’umma ba. Wannan halin da al’umma suka shiga, mu ma bai fi karfin zuwa kanmu ba tunda ya je kan wasu.
“Idan har zamu iya tallata ku cikin al’umma, ya zama dole mu fito mu sanar da ku tare da tunatar da ku idan kun kauce.”
A wani labari na daban, fitaccen malamin nan na jihar Sokoto, Malam Bello Yabo, ya fito a sabon bidiyo yayi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari tatas kan yadda yayi watsi da lamarin fasinjojin jirgin kasa da ke hannun ‘yan ta’adda.
A bidiyon da malamin ya saki a shafinsa na Facebook, ya sanar da cewa Buhari ya ci amanar ‘yan Najeriya kuma Allah zai tuhumesa saboda rantsuwa da yayi da Qur’ani kan cewa zai yi adalci.
Source:hausalegitng