Idan ‘ya’yan jam’iyyar APC ba su yarda da a yi sulhu a zaben fitar da gwani ba, to zabe ne kawai mafita.
Bisa dukkan alamu jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya na ci gaba da fuskantar baraka da rashin jituwa tsakanin jiga-jiganta kan babban taro na kasa da kuma zaben shuwagabannin jam’iyyar da ake shirin yi a ranar Asabar mai zuwa.
Tuni jam’iyyar ta kebe wa yankunan kasar mukamai daban-daban – inda misali aka kebe wa yankin arewa ta tsakiya kujerar shugaban jam’iyya na kasa.
Haka nan, shugaban kasar Muhammadu Buhari na kokarin ganin an kauce wa kada kuri’a wajen zaben shuwagabannin, a maimakon haka a sasanta tsakanin ‘yan takara, yayin da gwamnonin jihohi ke cewa za su goyi bayan duk wanda shugaba Buhari ya ce a ba kujerar shugabancin jam’iyyar.
To sai dai wasu kusoshin jam’iyyar sun bayyana cewa ba su yarda da wannan tsari ba, misali tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ya ce zai ci gaba da fafutikar neman kujerar shugaban jam’iyyar duk da cewa ba yankinsu ne aka kebe wa kujerar ba, kuma a ganinsa bai wa wani yanki ko wani mutum mukamin ba tare da zabe ba, rashin adalci ne.
To dazu bayan da gwamnonin jihohi na jam’iyyar ta APC suka gana da shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja, shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya yi wa wakilin BBC Ishaq Khalid karin bayani.
Sai ku latsa alamar lasifika a jikin hoton da ke ƙasa.