Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shirin N-Power da aka sauya wa fasalin zai samar da ayyukan yi akalla miliyan biyar ga matasa a kasar nan.
A cewar ministar harkokin jin-kai da yaki da fatara, Betta Edu, wadda ta bayyana hakan a gidan talabijin na Channels, ta ce shirin N-Power wani bangare ne na samar da tsaro da aka tsara don hana mutane fadawa cikin talauci.
Sarkin Kudan Ya Taya Mai Martaba Sarkin Zazzau Murnar Cika Shekara Uku A Karaga
Abubuwan Al’ajabi Da Abarba Ke Yi Wajen Gyaran Fata
“Muna aiki a kan matasan Nijeriya miliyan biyar masu shekaru tsakanin 18 zuwa 40 kuma za a dauki miliyan daya a kowace shekara. A kan shirin GEEP, muna aiki kan ‘yan Nijeriya miliyan 1.5,” in ji ta.
Kalaman nata ya zo ne kwanaki bayan da gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin na N-Power, wani bangare na shirin nan na ‘National Social Investment Programme (NSIP), wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a ranar 26 ga watan Yuni, 2016, domin yaki da matsalar rashin aikin yi da matasa ke fuskanta da kuma bunkasa zamantakewar al’umma.
Sai dai a cikin shirin da aka sauya wa fasalin, ministan ta jaddada cewa shirin N-Power zai kasance ne bisa tsarin farko-farko.
“Muddin kun cika ka’idojin kowane nau’i, za a ba ku dama. Don haka, ba lallai ne mu ware wa jihohi kaso ba,” in ji ministar.
Ta ce shirin da sauran shirye-shiryen shiga tsakani na gwamnati na da nufin yaki da talauci a kasar.
“Abin da ma’aikatarmu ke yi shi ne samar da hanyar kare lafiyar jama’a da ke hana wadannan mutane fadawa cikin talauci da kuma kokarin fitar da yawancinsu daga talauci.
“Mun tsara shirye-shirye daban-daban, shirye-shiryen kasa, wadanda ake sa ran za su magance matsalar talauci mai dimbin yawa. Tabbas muna da N-Power wanda ya kamata ya samar da ayyukan yi miliyan biyar a cikin shekaru biyar.
Ministar ya kara da cewa “Muna da wasu ayyuka da dama a kasa, dukkansu an yi niyya ne a fannoni daban-daban don yaki da talauci.”
Source LEADERSHIPHAUSA