Tun lokacin da aka sami wani malamin makarantar firamare da kashe dalibarsa, dan ya karbi kudin fansa, gwamnatin ganduje tace zai sa hannu kan hukuncin kisansa.
Ya kan Zama ban-barakwai, ko sabon batu ace yau gwamna ya sanya hannu kan dokar kashe mutum wanda kotu tayi.
A tsawon shekara bakwai da gwamna Ganduje yayi a matsayin gwmanan jihar Kano bai sanya hannu kan hukuncin kisa ko guda daya ba.
Kwamishinan Shari’a yace gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace zai sa hannu kan hukuncin rataya da kotu ta yankewa Mallam Abduljabbar.
kamar yadda Aminiya ta rawaito Yace: “Matsayar gwamna bai sauya ba kan sanya hannu akan hukunci da kotu ta yanke”
“Akwai matakan da ya kamata a bi kuma a shirye mai girma gwamna yake da zarar an kawo masa zai sanya hannu”
Kwamishinan ya ci gaba da cewa: “Babu wanda za a bari ya taka doka, kuma an dauki duk matakin da ya kamata a dauka”
“Mun gurfanar da Abduljabbar a gaban kotu ne domin bashi duk dama ta kare kansa, kuma Alhamdulillah kotu ta gamsu da hujjojin da muka gabatar shi yasa ta yanke masa hukunci”
A cewarsa hukuncin kotun ya wanke gwamnatin jihar Kano da ke nuna ba wani shafaffe da mai, sannan gwamnatin zata tabbatar da hakan bai sake faruwa ba.
Ganduje Ya Ce Zai Sanya Hannu Kan Hukuncin Kisa Ga Wanda ya Kashe Hanifa
An sami wani malamin makarantar wata daliba mai suna Hanifa da laifin dauke yarinyar tare da boyeta da zummar karbar kudin fansa a wajen mahaifanta. Sai dai kuma daga bisani malamin ya kashe dalibar tare da binne ta a makarantar da yake koyarwa.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta jagoranci wani atisaye da ya gano inda aka binne yarinyar tare da tonota.
An Gurfanar Dashi
A Gaban Kotu Bayan gurfanar dashi a gaban kotu wanda ake zargin ya musanta zargin da ake masa, amma da ga bisani kuma ya amsa.
Alkalin da ya jagoranci shari’ar ya yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga malamin su hanifa mai suna Abdul-Malik Tanko dan shima ya girbi abinda ya shuka.
Tuni dai gwamna Ganduje yace yana jiran fayil din yazo gaban sa dan ya sanya hannu dan zartar masa da hukuncin.
Source:LegitHausa