Malamai sun tofa albarkacin bakinsu a kan hukuncin da aka zartar a kan Abduljabbar Nasiru Kabara.
Sarki Yola, Alkalin kotun shari’a ya yanke hukuncin kisan-kai a dalilin batanci ga Annabi SAW ga shehin malamin.
Malamai da-dama sun yaba da hukuncin da kotun shari’a ta yi wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
A ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba 2022, kotun shari’a ta yanke hukuncin kisa ga malamin addinin nan, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta tattaro abin da wasu daga cikin malaman musulunci suke fada kan hukunci da Ibrahim Sarki Yola ya zartar.
Dr. Ibrahim Disina, shahararren malamin addinin Musulunci a garin Bauchi, yana cikin wadanda suka fara yada labarin, amma bai ce komai ba a kai.
Rabi’u Rijiyar Lemo wanda dama yana cikin manyan abokan adawar Malam Abduljabbar ya yi tsokaci a kan shari’ar, ya ce tun farko Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi kalaman batanci.
A cewar Dr. Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo, malamin ya gagara nuna inda lafazin ya zo a littafan musulunci, a karshe yake cewa gaskiya ce tayi halinta.
“Mutum ne ya yi kalaman Batanci ga Manzon Allah S.A.W kuma ya ce, wadannan kalaman suna cikin littattafan malaman Musulunci, ya ma ayyana sunayen wadannan littattafai, tare da juzu’i da shafi.
Aka nemi ya buda wadannan littattafai ya nuna inda wadannan kalamai suke amma ya gaza, sai ya koma kame-kame da cewa ai shi da ma’ana yake riwaya.
Ita ma ma’anar aka ce nuna lafazin da ya zo da wannan ma’anar shi ma hakan ya gagara.
Rabi’u Rijiyar Lemo Ranar farin ciki ga Muminai
Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto, babban bawahabiyen nan na Sokoto, ya ce jiya rana ce ta farin ciki ga muminai saboda an kare kimar Annabi SAW da sahaban sa.
“Rana ce da muminai suke murna da taimakon Allah’. Allah mun gode maka.
Ka kara kare martabar manzonka da iyalansa da almajiransa da masoyansa har ranar tashin alkiyama.
Ka tozarta, tare da wulakanta duk mai keta alfarmarsu. Alhamdu lillah” -Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto.
A bangaren Shehin Malami kuma limamin masallacin kasa Farfesa Ibrahim Maqari ya sha bam-bam, yana ganin banbamcin siyasa ya jawo aka zartar da wannan hukunci a kan Sheikh Kabara ba komai ba.
Ibrahim Maqari ya ce a tarihi, mafi yawan wadanda aka kashe da sunan zindiƙancin, ba shi ne asalin laifinsu ba, illa iyaka ana fakewa da wannan ne kurum.
“Mafi yawan waɗanda aka kashe saboda tuhumar zindiƙanci a tarihi idan mai karatu ya zurfafa bincike zai samu rikicin siyasa ne ya haɗasu da masu mulki…Amma ba zindiƙancin ne dalilin kisan ba.”
Source:LegitHausa