Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ba da tallafin Naira miliyan 100 ga ‘yan kasuwar wayar da Iftila’in gobara ya fadwa a Karamar Hukumar Damaturu a jihar.
Buni, ya ba da tallafin ne a ranar Laraba, a lokacin da ya ziyarci kasuwar domin jajanta wa ‘yan kasuwar.
Haka kuma ya umarci ma’aikatar ba da agajin gaggawa ta jihar da ta binciko yawan asarar da aka samu, domin ganin abin da gwamnatinsa za ta iya yi a kai.
Har ila yau, gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da ba da gudummawarsa ga ‘yan kasuwar.
A kwanakin baya ne dai kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa gobarar ta lakume kadarorin da yawan su ya kai kimanin Naira miliyan 130 a kasuwar Jagwal da ke Damaturu.

Source: LEADERSHIPHAUSA