A yayin da yajin aikin kungiyar malamai masu koyarwa na jami’o’i (ASUU) ya cika wata 4, daliban Najeriya sun koka da yadda karatunsu ya tsaya cak.
Daliban jami’ar da Legit.ng ta tattauna da su sun bayyana cewa gwamnatin tarayya bata musu adalci ba ta yadda karatunsu ya tsaya Daliban sun sanar da yadda suka koma zaman gida yayin da wasu suka fara sana’a domin dogaro da kansu a maimakon wannan jiran.
Yajin aikin kungiyar malamai masu koyarwa na jami’o’i (ASUU) ya ki ci balle cinyewa yayin da ya cika watanni hudu cif tun bayan fara shi a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022.
Har a halin yanzu, babu wata takamaiman magana ko wani yunkurin janye yajin aikin da kungiyar ke yi sakamakon nuna halin ko in kula da gwamnatin tarayyar Najeriya ta nuna musu.
Dalibai Sun Koka Kan Yajin Aikin Da Ya Ki Karewa, Sun Aike Sako ga FG. Hoto daga punchng.com Asali: UGC Legit.ng ta samu jin ta bakin wasu daliban jami’o’i kan yadda yajin aikin ya tsayar musu da karatunsa da kuma rawar da ya taka mai kyau ko akasin hakan a rayuwarsu.
A zantawar da Legit.ng tayi da wata dalibar jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria mai suna Yahanasu Khalid, cike da takaici ta sanar da yadda take hango kammala karatunta a shekarar nan amma abun yana neman zama mafarkin da ba zai zama gaskiya ba.
“Ni dalibar aji hudu ce da ke karantar ilimin aikin noma. A gaskiya daliban Najeriya mun shiga wani hali ganin cewa muna hango kammala karatu amma abun har yanzu shiru.
“Mun bata shekara daya tun farko sakamakon annobar korona. Mun dawo makaranta har na fara Project amma sai wannan yajin aikin ya ritsa da mu.
“Ya kamata gwamnati ta dube mu, kawayenmu da ke jami’o’in kudi duk sun kammala karatu. Mu ne aka bari a baya,” ta bayyana cike da takaici.
Sai dai dalibar ta ce ba ta yi zaman banza a gida ba koda ta koma. Ta saka kaji kuma har ta cire su, tana kokarin sake saka wasu na kiwon.
Ta kuma samu aiki a wata makarantar kudi inda take koyarwa domin zaman gidan ya isheta. “Don Allah gwamnatin tarayya ta dube mu, ta waiwayo ta biya bukatun ASUU, muna son komawa makaranta kafin mu tsufa a gida.
Daga dukkan alamu hankalin gwamnati yafi karkata kan zabukan nan dake karatowa, kuma mu ne dai masu kuri’ar,” ta kara da cewa Har ila yau, Legit.ng ta samu jin ta bakin Aisha Abdullahi, dalibar aji hudu a sashen ilimin zamantakewa a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, inda tace yajin aikin nan ya taba rayuwarta ta hanyoyi da dama.
“A gaskiya wannan yajin aikin ta wani fanni alheri ne. Ya bani damar zama in fahimci project dina saboda rubuta shi tare da karatu babban aiki ne a lokaci daya.
Na kara da mayar da hankali wurin karatuna balle wadanda na fara a farkon zangon karatu kafin a tafi yajin aikin.
“Yajin aikin nan yasa na koya tsara lokaci na. A matsayina na budurwa, ina fatan bayan kammala karatu in yi aure ne, toh zaman gidan nan ya bani damar iya kula da kannaina saboda mahaifiyata ta rasu watanni 8 da suka gabata kuma ni ce babba a gidanmu,” tace.
A bangare daya kuwa, Aisha ta koka kan yadda wannan yajin aikin ya tsayar da ita daga kammala karatunta wanda zai bata damar samun kwalin digirin. “A bangaren kwali, sakandare zan ce nake da ita.