Gwamnatin Kano ta ce, ta sake dawo da ma’aikata 9332 cikin wadanda ta dakatar da albashinsu sama da 10,000 bayan an tantance su.
Bayan daukar watanni biyu ana tantance ma’aikatan da gwamnatin ta dakatar sama da 10,000 da Gwamnatin Ganduje ta dauka aiki yanzu ta amince da mayar da guda 9,332.
Da yake bayyana sakamakon kwamitin tantancewar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa, Sakataren Gwamnatin Jihar, Dr. Abdullahi Bichi, ya ce, an amince da mayar da wadanda suka cancanta bakin aikinsu.
Cewar Bichi a ranar Juma’a a Kano, ya ce daga cikin wadanda gwamnatin Ganduje ta dauka aiki ta hanyar da ba ta dace ba akwai wata yarinya ‘yar shekara 13, wanda yin hakan ya saba wa ka’idar aikin gwamnati.
Sauran abubuwan da aka yi wadanda ba su dace ba sun haɗa da daukar wadanda ba su kammala hidimar kasa ta NYSC ba, da wadanda ba su kammala karama da babbar Sakandare ba da daukar wasu da aka dauke su aka tura su wuraren da ba su cancantar ba.
Tun a baya gwamnatin Abba Kabir ta dakatar da ma’aikatan su kimanin 12,566 aiki bisa zargin tabka wasu kura-kurai da aka samu yayin daukar aikin.
Source: LEADERSHIPHAUSA