Kungiyar ’yan jarida masu bibbiyar harkokin wasanni ta duniya wato AIPS, ta fitar da kayayyakin aikin jarida mafiya burgewa a shekarar 2022 da ’yan jaridar suka zaba ta hanyar jefa kuri’a, kuma gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta kai matsayi na farko a wannan fage.
A yayin zabe na wannan karo, sassan uku na farko a samu kuri’un, su ne gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, da “cikakkiyar” gasar wasanni ta cin kofin Turai da aka yi a birnin Munich.
Gasar wasannin ta kunshi wasanni tara, da suka hada da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, da wasannin motsa jiki, da tseren kekuna, da wasan kwallon tebur da sauransu.
Ta ukun kuwa ita ce gasar wasannin kasashe renon Ingila ko “Commonwealth” wadda ta gudana a birnin Birmingham.
AIPS ta bayyana a kan shafinta na yanar gizo cewa, a shekarar 2022, yawancin kayayyakin aikin jarida da aka yi amfani da su a wasannin suna da kayatarwa sosai, kuma gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, da aka gudanar.
A farkon shekarar 2022, ita ce mafi burgewa a cikinsu, sabo da an gudanar da wannan cibiyar watsa labarai ta gasar kamar yadda ’yan jaridu suke fata, har ma ta ba da hidima mai gamsarwa. (Safiyah Ma)