Jaruman yan kwallon kungiyar kwallon Najeriya wato Super Eagles za su kaddamar da yakin neman zaben Tinubu a Kano.
Baffa Babba Dan’Agundi, shugaban kungiyar kungiyar Tinubu/Shettima campaign support group ya sanar da hakan.
Dan’Agundi ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ne zai zama babban bakon a wurin taron da aka fatan yan tsaffin yan kwallon za su bukaci masoyansu su zabi Tinubu da Shettima.
Yan kwallon Super Eagles, za su kaddamar da yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, a jihar Kano, rahoton Independent.
Direkta Janar na kungiyar Tinubu/Shettima campaign support group, Baffa Babba Dan’Agundi, a ranar Talata, ya ce yan takarar jam’iyyar na majalisar tarayya a mazabar Dawakin Tofa/Rimingado/Tofa, Abba Umar Ganduje zai tarbi tsaffin jaruman yan kwallon a ranar 10 ga watan Disamba.
Dan’Agundi ya ce jaruman za su taka rawa wurin kira ga magoya bayansa da masoyansu a fadin kasar su zabi Tinubu da abokin takararsa Kashim Shettima, Daily Trust ta rahoto.
Ya kara da cewa: “Shugaba Muhammadu Buhari zai zama babban bako na musamman a wurin taron.”
Direktan ya kuma ce an yi nisa a shirye-shirye tare da kwamitin shirye-shirye na jihar Kano tare da amincewar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Idan za a iya tunawa matasa da kungiyoyin bada tallafi na dan takarar shugaban kasa na APC a baya-bayan nan sun yi tattaki na mutum miliyan 1 a jihar.
Sai dai kwararrun masu nazarin harkokin zabe sun ce jihar har yanzu da wuya a iya cewa ga jam’iyyar da za ta ci jihar cikin manyan yan takarar shugaban kasa.
A wani rahoton, dubban matasa sun fito kwansu da kwarkwata a tinunan jihar Kano domin nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
Matasan sun fara tattaki ne daga fadar mai martaba sarkin Kano har zuwa gidan gwamnatin jihar Kano, sannan daga baya suka shiga taro, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
A jawabin da ya yi wurin taron, Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano ya ce ganin irin dandazon matasan da suka fito alama ce da ke nuna Tinubu ya lashe kuri’un Kano a zaben 2023.
Source:Legithausa