Dan wasan kwallon jafa na Juventus da Faransa, Paul Pogba, ya bayyana cewar ya kamu da cutar hawan jini bayan gwajin da aka yi masa na kwayoyi bayan Juventus ta doke Udinese da ci 3-0 a gasar Seria A a watan jiya.
An kira Paul Pogba ne domin yin gwaji bayan Juventus ta lallasa Udinese da ci 3-0 a ranar 20 ga watan Agusta.
Dan wasan mai shekaru 30 bai buga wasan ba inda koci Massimiliano Allegri ya ajiyeshi a benci.
Gwajin ya nuna alamun testosterone masu kara kuzari a jikin Pogba.
A cewar rahotanni daban-daban, yanzu za a duba samfurin gwaji na biyu don tantance sakamako.
Idan har aka tabbatar da Pogba ya sha kwayoyi masu kara kuzari.
Kotun hukunta masu shan kwayoyin kara kuzari ta kasa,za ta hukunta Pogba kuma zai iya fuskantar dakatarwar shekaru biyu daga wasan kwallon kafa.
A wani labarin na daban Shugaban hukumar kwallon kafar Spain, Luis Rubiales, ya yi murabus daga mukaminsa, sakamakon sukar da aka yi masa na sumbatar Jenni Hermoso a lebe a wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta mata.
Tuni dai aka dakatar da Rubiales,ya aika da takardar murabus dinsa zuwa ga shugaban riko na hukumar.
A wata budaddiyar wasika,Rubiales ya bayyana matakinsa na sauka daga karshe a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin.
Nayi murabus ne saboda ba zan iya ci gaba da aiki na ba in ji Rubiales a cikin wata hira da gidan talabijin.
An bani shawarar cewa ina bukatar in mai da hankali ga mutuncina kuma in ci gaba da rayuwata inji Rubiales.
Source: LEADERSHIPHAUSA