Kungiyar Kasashe asu arzikin man fetur ta Opec da kawayenta sun amince da ci gaba da hakar yawan danyen man fetur din da kasashen ke fitawar a kullum kamar yadda yake ba tare da kari ko ragi ba.
A cewar kungiyar mai halastattun mambobi 13, yaduwar annobar Corona ta shafi dukkanin harkoki na duniya a don haka babu damar kara yawan gangunan man fetur din da kasashen ke hakowa kowacce rana, amma dai za a iya barin shi yadda yake, kasancewar ya yi dai-dai da bukatar mambobin kungiyar.
A bara dai kungiyar ta amince ta kara yawan gangunan da kasashen ke fitarwa kowacce rana a bana, amma da alama hakan ba zai yiwu ba kasancewar cutar na ci gaba da banna.
Sai dai kungiyar ta kuma ce zata ci gaba da bibiyar wannan mataki yayin da duniya ke ci gaba da yunkurin shawo kan cutar Corona da nufin kara yawan gangunan fetur din da ake hakowa kowacce ranar tskaanin mambobin kungiyar.
A wani labarin na daban Kungiyar kasashe masu arzikin mai OPEC ta ce Najeriya da sauran kasashe masu tasowa za su amfana da kimanin dalar Amurka biliyan 450 da za a kashe wajen gina sabbin matatun mai da kuma bunkasa ayyukan wadanda suke da su.
OPEC ta ce zuba jarin wani bangare a karkashin gagarumin shirin da take jagoranta, da ya kunshi dala tiriliyan 1 da biliyan 500, da za a zuba a bangaren mai da iskar gas domin bunkasa fanonin daga 2021 da muke ciki zuwa shekarar 2045.