Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana aniyar karbar bakuncin wasannin motsa jiki na Olympics da za a gudanar a shekarar 2036.
Wannan bayyana sha’awa a Qatar na fitowa ne daga kwamitin kula da harkokin motsa jiki na kasar, kamar yadda ya wallafa a shafin Twitter.
Kwamitin ya ce ya mika bukatar ne ta farko ga kwamitin shiya wasannin Olympics ta duniya don amincewa da bukatar Qasar, rahoton Marca.
Wannan zai ba kwamitin na duniya duba yiwuwar ba Qatar dama ko hana ta karbar bakuncin wasannin da za a gudanar nan da shekaru kusan 12 masu zuwa.
India da Indonesia na neman irin wannan dama
A bangare gudan kasashen nahiyar Asia; India da Indonesia sun bayyana sha’awar karbar bakuncin wasannin na Olympic da za agudanar, BBC Hausa ta ruwaito.
Gasar da aka kammala ta cin kofin duniya ta zo wa da kasar Qatar da alherai da yawa ta kudaden shiga, a tun farko kasar ta yi hasashen samun akalla dala biliyan 20 bayan kammala wasanni.
Hangen irin wannan ribar ne ta sa kasar ta Qatar ke kara sha’awar karbar bakuncin wasan duniya; a wannan karon wasannin motsa jiki na Olympic.
Ba wannan ne karon farko da Qatar ta fara neman karbar bakuncin wasan Olympic ba, a shekarun 2016, 2020 da 2032 ta nemi irin wannan bukata, amma kwamitin ya ki amincewa.