Matashin dan wasan gaban Fc Barcelona Marc Guiu ya shigo wasan da Barca ta doke Bilbao a mintunan karshe na wasan.
Amma ya nuna dalilin da yasa Kocin Barcelona Xavi Hernandez ya dauko shi daga karamar kungiyar ta Barca ya saka shi a wasansa na farko ga kungiyar.
Guiu ya shigo a lokacin da ake bukatar taimako kuma ya baiwa marada kunya ta hanyar jeda kwallo daya tilo da tayi sanadin da Barcelona ta samu nasara akan Bilbao.
A wani labarin na daban babban dan kasuwar Kasar Katar Sheikh Jassim bai yi nasara ba a yunkurinsa na sayen Manchester United amma rahotanni sun nuna cewar ya shiga tattaunawa domin mallakar wani kulob na Premier.
Sheikh Jassim ya janye daga neman karbe ragamar Manchester United amma dan kasuwar dan kasar Katar na sha’awar saka hannun jari a Tottenham.
Sheikh Jassim ya kasance daya daga cikin wadanda suka nuna sha’awar mallakar Man Utd tare da Sir Jim Ratcliffe tun bayan da masu kungiyar Glazer Family suka saka ta a kasuwa a watan Nuwambar bara.
Ratcliffe yanzu ya shirya don sayen kashi 25 cikin 100 na kulob din tare da tunanin zuwa gaba zai samu cikakken iko na mallakarta gaba daya.
Duk da cewar Sheikh Jassim bai samu damar saye Manchester United ba amma ya nuna cewar har yanzu yanada sha’awar saka hannun jari a Premier League.
Katar ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya na bara amma sun ga abokan hamayyar yankin Saudi Arabiya da Abu Dhabi sun samu gindin zama a gasar Premier ta hanyar saye kungiyoyin Newcastle da Manchester City.
Kuma an yi imanin cewa manyan ‘yan kasuwar kasar Katar suna da sha’awar saka hannun jari a kulob din Ingila.
Shugaban Paris Saint-Germain Nasser Al-Khelaifi ya taka rawa a yunkurin da Sheikh Jassim ya yi na sayen United.
Wani rahoto a farkon wannan shekarar da jaridar ‘The Athletic’ ta fiyar ya bayyana yadda, a wani bangare na tayin sa na sayen United, da farko tawagar Jassim ta tuntubi Al-Khelaifi don neman shawara kan kimar United, bayan da Glazers ta bukaci fam biliyan 6.4 ga kulob din.
Zuwa yanzu tawagar Sheikh Jassim ta gana da shugaban Tottenham Daniel Leby don tattaunawa akan yuwuwar saka hannun jari a kungiyar.
Idan hakan ta tabbata kenan Jassim zai cika burinsa na sayen daya daga cikin manyan kungiyoyi masu daraja a Duniya.
Source LEADERSHIPHAUSA