Lampard ya amince da zama kocin Everton
Tsohon tauraron dan kwallon Chelsea kuma tsohon kocin kungiyar Prank Lampard ya amince ya zama kocin Everton.
Lampard ya amince da aikin na shekaru 2 da rabi.
Dan shekaru 43 dai ya samu aikin ne bayan da aka musu tantancewa su 3.
Lampard ya maye gurbin Rafael Benitez ne wanda ya bar kungiyar.