Al’umomin jihar Barno dake Najeriya sun ce har ya zuwa yanzu babu labarin dalibai mata 110 daga cikin 276 da mayakan boko Haram suka sace a Sakandaren Chibok a shekarar 2014.
Wata kungiyar da ake kira Kibaku ta raya Yankin Chibok, wadda ke sahun gaba wajen fafutukar ganin an ceto Yam matan ta hannun shugaban ta Dauda Iliya tace daga cikin daliban 276, 57 sun yi nasarar gudu daga hannun wadanda akayi garkuwa da su.
Shugaban al’ummar yace daga karshen shekarar 2018 zuwa yanzu, mayakan book haram sun zafafa hare haren su a yankin, ciki harda wanda aka kai kautikari a ranar 14 ga wannan wata inda aka sace Yam mata 5 tare da kasha mutane 3 da kuma kona gidaje da mujami’u.
A wani labarin na daban Gwamnatin Jihar Barno dake Najeriya ta haramta sayar da gawayi da kuma itace a titunan birnin Maiduguri a wani shirin rage yawan itatuwan da ake sarewa domin yin girki a yunkurin ta na kare muhalli.
Kwamishinan shari’ar Jihar Kaka-Shehu Lawal ya bayyana haramcin wajen bikin dasa itatuwa da aka gudanar yau wanda yayi daidai da ranar bikin kare muhalli ta duniya.
Lawal yace gwamnatin Barno ta jagoranci shuka itatuwan neem sama da miliyan guda a fadin jihar, yayin da ya bayyana aniyar su ta goyawa kungiyoyi masu zaman kan su da hukumomi baya domin shuka itatuwa a jihar.
Mataimakin Gwamnan Jihar Umar Usman Kadafur da ya halarci bikin yace an shuka nau’oin itatuwa daban daban har 5,000 a jihar, yayin da za’a shuka wasu Karin 500,000 a yankunan ta baki daya.
Jihar Barno na daya daga cikin jihohin dake fama da matsalar kwararowar hamada, yayin da jama’ar ta ke cikin wadanda ke sare itatuwa domin yin girki.