An kammala Gasar Olympics Ta Lokacin Hunturu A Birnin Beijing Na Kasar China.
Kimanin yan wasa 3,000 ne suka fafata a wasanni 109 a tsawon mako biyu da aka kwashe ana gudanar da gasar. Shugaban hukumar da ke shirya gasar Olympics ta kasar Thomas Bach, ya yi kira ga yan siyasa a fadin duniya da su dauki darasi daga irin yadda yan wasan suka nuna sadaukarwa da kuma rungumar zaman lafiya.
Har ila yau ya kara dda cewa Abin da ya hada mu a wasannin Olympics ya fi karfin abinda ya yi kokarin raba mu” wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tada jijiyar wuya tsakanin Rasha da Yukren.
Thomas ya kuma shawarci kasashe da su cigaba da yi wa al’umma allurar rigakafi ta Covid-19. Yace Matukar” muna son kawo karshen wannan annoba to dole ne mu saki jiki mu cigaba da daukar matakai da suka dace
Gasar ta fuskanci rudani, a lokacin da kotun da’ar wasanni ta wanke yar kasar Rasha Kamela Valieva duk da kamata da laifin shan kwayar kara kuzari da aka haramta.