Sarauniya Elizabeth Ta Ingila Ta Kamu Da Cutar corona.
A sanarwar da fadar Buckingham ta fitar an bayyana cewa sarauniya na tattare da alamun sanyi amma ana sa ran za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta sama-sama a mako mai zuwa.
“Za a ci gaba da duba lafiyarta kuma za a bi duka hanyoyin da suka dace,” kamar yadda fadar ta bayyana a sanarwa yau Lahadi.
Sarauniya Elizabeth mai shekara 95 ta hadu da babban danta kuma magajinta wato Yarima Charles wanda shi ma ya kamu da corona a makon da ya gabata.