Kamar yadda gidan njarida na Press T.v ta nakalto, ‘yan wasan na olympic wadanda suka fito daga kasashe mabambanta sun nuna kin amincewa su kara wasan na olympic da dan wasan haramtacciyar kasar isra’ela domin nuna goyon bayan su ga raunana falasdinawa da haramtacciyar kasar isra’elan ke kashewa a kullum a bangare guda kuma su nuna kyama ga kasar ta isra’ela wacce take bisa haramci gami da saba ka’ida.
Dan wasan kasar sudan Muhammad Abdulrasool ya kauracewa wasan yayin da ta bayyana zai kara da Butbul na kasar isra’ila, yayin da Muhammada Abdulrasool ya bayyana cewa bazai shiga wasan da bayahuden isra’ilan ba a dai dai lokacin da isra’ilan take tsaka da zaluntar al’ummar falasdinawa tana korar su daga gidajen su.
Amma sai dai hukumar olympic ta duniya tayi kokarin boye dalilin da yasa Muhammad Abdulrasool wanda ya samu maki mafi girma a gasar kuma ake sa ran zai lashe gasar yaki bayyana domin fafatawa da dan wasan kasar yahudawan isra’ilan, amma sai dai Muhammad Abdulrasool bai boye dalilin sa na kauracewa wasan ba inda ya bayyana kyamatar zalunci gami da take hakkin dan adam da isra’ilan ta shahara dashi cikin dalilan sa na kin amincewa ya fafata da Batbul na isra’ilan.
Ba Muhammad Abdulrasool na sudan kadai ba Fethi Nourine na kasar Algeria ma dai nuna kin amincewa ya kara da dan wasan isra’ilan yayi, bayan da Muhammad Abdulrasool ya janye sai aka bukaci Fethi Nouri ya kara da Batbul na isra’ila inda shima ya kekasa kasa yace ba dashi ba abinda ya janyo hukumar olympic din ta kore.
Fethi Nouri ya bayyana gwamma a kore shi daga gasar da ya fafata wasa da dan wasan haramtacciyar kasar isra’ila.
A halin yanzu dai kusan gabadayan ‘yan wasan na olympic sun ki amincewa su kara da isra’ila amma sai dai ana jiran sati mai kamawa domin ganin ko ‘yan wasan saudiyya zasu yadda su kara da ‘yan wasan haramtacciyar kasar isra’ilan ko a’a?