Kamar yadda rahotanni suke ishe mu daga jihar kaduna ya tabbatar mana da cewa yau ashirin da takwas watan yulin shekarar dubu biyu da ashirin da daya an cigaba da sauraron shari’ar jaagoran mabiya mazhabar shi’a na afirka da mai dakin sa a wata karamar kotun jihar kaduna.
Rahotanni sun tabbatar mana da cewa tun da farko lauyoyin kowanne bangare sun samu halartar kotun a kan lokacin inda ake sa ran alkalin kotun zai yanke hukunci a bisa bukatar ”NO CASE SUBMISSION” da lauyoyin malam zakzaky suka gabatar a gaban sa, sakamakon rashin iya alakanta malamin da laifukan da ake tuhumar sa da shaidun masu kara ma’ana bangaren gwamnatin kaduna sukayi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yau shehin malamin ya samu halartar kotun domin sauraran hukuncin da kotun zata yanke dangane da dadaddiyar shari’ar da aka jima ana sauraron yadda zata kasance.
Ita dai gwamnatin jihar kaduna ta shigar kasar jagoran da shi’a bisa zargin tunzura magoya baya wajen aikata ayyukan da suka hada da kisan wani babban soja a kaduna, amma sai dai abinda ya shige ma mutane duhu shine wadanda ake zargin malamin ya tunzura tuni babar kotu a kadunan ta wanke su daga aikata wadancan laifuka amma kuma yanzu anzo ana tuhumar malam zakzaky da laifn tunzura magoya baya su aikata laifin da kotu ta tabbatar bai faru ba kuma ba’ayi shi ba.
Dadi a kan wannan kafin wannan shari’a dama dai a kwia hukuncin babbar koatun tarayya wacce ta wanke jagoran mabiya mazhabar shi’a din har ma tayi umarnin a biya shi diyya kuma a gina masa gida a indaya zaba a fadin.
Rahotanni dai daga kotun suna tabbatar da cewa zaman na yau ya fara gudana amma zuwa yanzu lokacin da muke hada muku wannan rahoto kotun ta tafi hutu.
Ana sa ran bayan dawowa hutun kotu zata yanke hukunci bisa bukatar da lauyoyin malamin suka shigar na ”NO CASE SUBMISSION” amma sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa lauyan gwamnati bayero dari ya fice daga kotun amma yace zai dawo kafin karewar lokacin hutun.