Tsohon Gwamnan Jihar Rivers yace a shekarun da suka gabata, za ka ga mutane sun zama attajirai dare daya ba tare da an san su da wata sana’a ba, kuma babu wanda ya hukunta su, amma a karkashin mulkin Buhari ba’a samun haka.
Rotimi Amaechi yace cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a karkashin gwamnatocin Najeriya da suka shude, ta yadda za ka ga mutane suna bushasha da dukiyar da ba’a san inda suka samo ta ba a bainar jama’a, amma a karkashin wannan gwamnati idan za kayi sata sai dai kayi ta a boye, kuma idan an kama ka, zaka fuskanci fushin hukuma.
Wannan matsayi na ministan a hirar da yayi da jaridar Daily Trust na zuwa ne a daidai lokacin da wasu Yan Najeriya ke zargin cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar wasu daga cikin jami’an gwamnatin san a facaka da dukiyar jama’a.