Ministan Buhari ya shiga ganawa da masu ruwa da tsaki a harkar samar da wutar lantarki a Najeriya, sakamakon dauke wuta a duk fadin kasar.
Wannan na zuwa ne bayan da aka samu baraka a wutar lantarki a yau Litinin, lamarin da ya tunzura ‘yan kasar Ministan ya bayyana manufar zaman, inda yace neman mafita aka zo ba daurawa wani laifi ba a yanzu.
Ministan wutar lantarki Engr. Abubakar D. Aliyu ya shiga ganawar gaggawa da masu ruwa da tsaki a harkar samar da wutar lantarki domin magance karancin wutar lantarki da ke haifar da matsalar dauke wuta a fadin kasar nan.
Daily Trust ta rahoto ministan yana gargadin cewa dole ne masu ruwa da tsaki su hada kai don ganin an samu mafita ga matsalr wuta.
Ministan Buhari ya kira taron gaggawa | Hoto: dailytrust.com Source: UGC Taron wanda ya gudana a dakin taro na ma’aikatar wutan lantarki, ya samu halartar tawaga daga kamfanonin samar da wutan lantarki naTCN, NBET, NDPHC, NNPC, Shell da sauran masu ruwa da tsaki a harkar wutar lantarki.
A rahoton Vanguard da Legit.ng Hausa ta tattaro, ministan ya bude taron da cewa: “An kira wannan taro ne domin magance matsalar wutar lantarki a kasar nan da muke ganin ba a ji dadinsa ba. “
Dole ne mu nemo mafita ta yadda ‘yan Najeriya za su samu wutar lantarki.
Ina so mu yi hakuri mu tattauna da juna, ba wai muna zargin junan mu ba”. dangane da dauke wutar lantarkin.
Aliyu ya ci gaba da cewa, gwamnatin Najeriya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an samu ci gaba a fannin samar da wutar lantarki ba kana da da inganta samuwarsa a fadin kasar ba.
A taron a cewar ministar, za a samar da hanyoyin da za su tabbatar da magance duk wasu matsalolin da suka shafi samar da wutar lantarki a Najeriya cikin gaggawa.
Manyan kayan abinci uku da farashin su ya yi tashin gwauron zabi a kasuwar Legas A wani labarin, abubuwan dake faruwa a fadin duniya na cigaba da shafar kayan masarufi a Najeriya, a cewar yan kasuwa.
A wani bincike da Legit.ng ta gudanar a wata babbar kasuwa a Najeriya, mun gano cewa farashin kayan abinci bashi da tabbas kuma samun su ya kara wahala.
Kamar Wake, Shinkafa da Gari, farashin ya sauka da sama da kashi biyar cikin dari yayin da kayan Masarufin da ake cikin kakarsu suka kara tashi.