Labarin karya dangane da rayuwar babban sakataren kungiyar neman ‘yancin nan dake a kasar labanan sayyid hassan nasrullah ya watsu a kafafan sada zumunta na zamani.
Labarin na karya ya watsu ne a dalilin tari da shugaban na hisbullah yayi a wata fira ta kai tsaye da akayi dashi a gidan talabijin kuma daga nan ba’a kuma jin muryar sa ba wanna yasa wasu bata gari suka fara, yada labarin shugaban na hisbullah baya raye, wanda hakan a ta bakin wadanda abin ya shafa sam karya ne babu kamshin gaskiya dangane da wannan labari.
”Sayyid hassan Nasrullah yana raye kuma yana cigaba da gudanar da ayyukan sa kamar yadda ya saba gudanarwa sabanin yadda bata gari suke yadawa a kafafen sada zumunta na zamani” cewar wani na kusa da Nasrullah.
Masu yada wancan labari na karya suna cewa wai sayyid hassan nasrullah ya kamu da cutar korona kuma ya mutu a lokacin da ake masa magani, wannan tasa kungiyar ta hisbullah ta sanar da karyata wancan labarin.
Majiyar mu tace kungiyar hisbullah ta tabbatar da cewa zuwa yanzu babu wani mamba na kungiyar daya kamu da cutar korona balle har ta kai ga sanadin rayuwar sa.
Kungiyar ta kara da cewa shugaban nata sayyid hassan nasrullah yana nan raye kuma cikin koshin lafiya , yana kuma cigaba da gudanar da ayyukan sa kamar yadda ya saba.
Kafofin sadarwa daga labanan sun sanar da karyata wannan labari kamar kafar sadarwa ta ”lebenon newa agency” da sauran su.
https://twitter.com/sultanaeljoufi/status/1399167816083906561?s=20
‘AJ News Club’
So True … So The Best!
Follow Us: @ajnewsclub 🍀 pic.twitter.com/HfGCCa2KQm— AJ News Club (@ajnewsclub) May 18, 2021
Kamar yadda kafar sadarwa ta Aljoumhuriyya ta tabbatar tace sayyid hassan nasrullah yana nan a raye kuma yana lafiya sa’annan yanayin sa ya kara zama da kyau sosai a kan yadda aka ganshi a karshe kuma yana nan yana cigaba da sabgogin sa na yau da kullum.
Majiyar ta kuma tabbatar da cewa masu son ganin wani abu mara dadi ya samu shugaban na hisbullah su sani sarai cewa babu abinda ya same shi kuma wannan yana nuna irin tasirin Hassan Nasrullah din da kuma yadda kungiyar ta hisbullah ta samu tagomashi a gabashin asiya dama duniya baki daya.