A ranar asabar 17 ga watan July 2022 shugaban kasar Amurka Joe Biden ya gana shugabannin larabawa a taron ”GCC+ 3 summit” a Saudiyya.
Biden wanda ya isa Saudiyya ya samu ganawa da yariman Saudiyyan Muhammad Bn Salman kuma ya gana da sarkin Saudiyyan Salman Bn Abdulazeez duk a wani salo na tabbatar da bukatun amurkan a nahiyar gabas ta tsakiya.
Manazarta na ganin dabarar taron GCC+ 3 summit da Biden yayi amfani da ita ba wani abu bane illah samar da hanya mafi sauki domin ya samu tattaunawa ta kai tsaye da shugabannin larabawa dangane da samar da alakokin da zasu kawo karshen matsalolin da suka sanyo amurkan a gaba sa’annan kuma ya bama Iran amsa dangane da tasirin da ta samu a nahiyar gabas ta tsakiya.
Shugabannin larabawan da Biden ya samu ganawa dasu sun hada da shugabannin Saudi Arabia, Kuwait, United Arab Emirates, Qatar, Bahrain da Oman da kuma Egypt, Iraq da Jordan.
An kuma assasa wannan kungiya ne ta shugabannin kasashen larabawa masu arzikin man fetur domin samar da hanyoyin da za’a inganta gami ribanya danyen man fetur din da za’a dinga fitarwa kasuwannin duniya wanda wannan itace babbar matsalar da ta sha kan amurka a halin yanzu.
Ana dai iya cewa shugannin larabawan suna so su nuna sun gujewa Iran wacce itace babbar abokiyar adawar amurkan a duniya kuma sun koma bayan amurka wacce suke da bambancin addini,tarihi gami nahiya da ita sakamakon bukatun kashin kai.
A firar da kafar sadarwa ta Press T.v tayi da masanin tahiri kuma mawallafi Marcus Papadopoulos ya bayyana kasashen larabawa musamman Saudiyya a matsayin wanda basu damu da lamarin Falasdinawa da musulmi gabadaya ba, sakamakon yadda suke hada kai da kasashen dake zaluntar musulmi irin su amurka da kuma haramtacciyar kasar isra’ila.
A wani labarin kuma duk da musanta hannu a kisan kashshogi da yariman saudiyya bn salman yayi amma shugaba biden na amurka ya gargade shi a kada ya kuskura ya kuma maimaita irin kuskuren da yayi na kisan kashshogin.